Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ambaliyar Ruwa Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 8 A Iraqi

Daga Umar Shuaibu Zuwa yanzu, akalla mutane takwas ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ruwan sama mai karfi ya ha...


Daga Umar Shuaibu

Zuwa yanzu, akalla mutane takwas ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ruwan sama mai karfi ya haddasa a garin Erbil dake yankin Kurdistan a Kasar Iraki da safiyar a yau Juma'a 17/12/2021. Wasu mutane hudu kuma sun jikkata kamar yadda Gwamnan Erbil ɗin Omid Khoshnaaw ya shaidawa AFP. 

Omid ya bayyana cewa, an fara ambaliyar ne da misalin karfe 4.00 na asuba agogon ƙasar, kuma ta yi sanadiyar mutuwar mutum takwas ciki har da mata da ƙananan yara. Sannan ambaliyar ta haddasa asarar dukiya mai yawa. 

Ya kara da cewa, masu ba da agajin gaggawa hudu ne suka jikkata bayan ruwan ya tafi da motar su a lokacin da suke kokarin ceto rayuwar 'yan kasar. 

Mai magana da yawun 'yan agajin a Erbil, Sarkot Karach ya shaidawa AFP cewa, ɗaya daga cikin mutane takwas da suka mutu ya rasa ransa ne sakamakon tsawa da ta sauka a kan shi, sauran mutane bakwai din kuma sun nutse ne a gidajen su. 

Ya kara da cewa, har yanzu akwai mutanen da ba a gani ba, saboda haka adadin mutanen da suka mutu zai iya ƙaruwa. 
Akwai kuma 'yan kasar da aka tilastawa fita daga gidajen su. Asarar dukiyar da akayi ma ta munana.

No comments