Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

BIDIYO: An Bawa Hammata Iska A Majalisar Turkiyya

  Daga Umar Shuaibu Fadan ya biyo bayan sukan da Ministan Harkokin cikin gida na Kasar Turkiyya Suleyman Soylu ya yi wa mataimak...


 
Daga Umar Shuaibu

Fadan ya biyo bayan sukan da Ministan Harkokin cikin gida na Kasar Turkiyya Suleyman Soylu ya yi wa mataimakin shugaban Jam'iyyar adawa a majalisar. 

Mista Erkan Aydin, mataimakin shugaban Jam'iyyar adawa ta (CHP) yana jawabi ne a kan kasafin kudin kasar na shekarar 2022, ɓangaren da ya shafi ma'aikatar harkokin cikin gida da kuma ma'aikatar Fasaha da ƙere-ƙere jiya Laraba 8 ga watan Disamba 2021 a majalisar. 

A cikin jawabin na shi ya tambayi Ministan Harkokin cikin gida na Kasar Mr Soylu cewa me yasa yake amfani da jirgi mallakin wani fitaccen Ɗan Kasuwa da ake zargi da halatta kudin Haram. 

Aydin ya kuma nuna wa taron majalisar hoton ministan a cikin Jirgin wanda hakan ya ƙara fusata ministan. 

"Ƙarya kake yi! Kai makaryaci ne!" Mr Soylu ya faɗa a fusace. 

Daga nan ne faɗa ya ɓarke tsakanin 'yan jam'iyyar adawa ta CHP da 'yan jam'iyyar AKP masu rinjaye a majalisar. 

Faɗa a majalisar kasar Turkiyya dai ya zama tamkar ruwan dare cikin kwanakin nan, kusan ko wani magana a majalisar na iya sa wa a ba wa hammata iska nan take. 

Ko a watan da ya gabata, an yi ta faɗace-faɗace yayin tattaunawa a kan kasafin kudin kasar na shekarar 2022, musamman a maganar da suka shafi kasafin ɓangaren ma'aikatan harkokin cikin gida.

Ga Bidiyon dambacewar;

No comments