Kasa da shekaru 4 bayan cire haramcin zuwa gidajen sinima da gwamnatin Saudi Arabia ta yi, kasar ta shirya wani kasaitaccen biki...
Kasa da shekaru 4 bayan cire haramcin zuwa gidajen sinima da gwamnatin Saudi Arabia ta yi, kasar ta shirya wani kasaitaccen biki a birnin Jeddah domin karrama fitattun masu shirin fina finan duniya irin sa na farko a tarihin kasar.
Masu shirin fina finai daga Saudi Arabiya da kasashen Larabawa da kuma kasashen duniya suka mamaye wurin bikin, wasu daga cikin su sanye da kayan kawa irin na kasashen duniya sabanin abayar da aka saba ganin matan Larabawa suna sanyawa.
Daraktan shirya bikin Mohammed Al Turki ya bayyana yau a matsayin babbar ranar tarihi ga Masarautar Saudiya.
Ita dai Saudi Arabiya ta haramta gidajen nuna fina finai ko kuma sinima na shekaru da dama, har sai a watan Afrilun shekarar 2018 aka bude su ga jama’a.
Yayin gudanar da wannan biki da bude yau, ana saran masu shirin fina finan da daraktoci zasu kwashe kwanaki 10 suna nuna bajintar su a birnin Jeddah.
Masu shirya bikin sun ce za’a kwashe wadannan kwanaki ana nuna fina finai 138 daga kasashe 67 da akayi a cikin harsuna 30.
Daga cikin wadannan fina finai akwai ‘The Alleys’ da Bassel Ghandour ya jagoranta da ‘Cyrano’ na Joe Wright da kuma ‘83’ da akayi akan nasarar kasar India a gasar cin kofin duniya na kurket a shekarar 1983.
Ana saran bikin ya karrama Haifaa al-Mansour, mace ta farko ‘Yar kasar Saudiya da ta shirya shirin ‘Wadjda’ a shekarar 2021, abinda ya bata damar lashe kyaututtuka da dama a kasashen duniya.
Mutane da daman a kallon sauyin da ake samu a kasar Saudi Arabiya da nasarar da Yarima Mohammed bin Salman ya samu na zama Yarima mai jiran gado a shekarar 2017.
Wannan bikin na zuwa ne kwana guda bayan kammala bikin tseren motocin duniya da akayi a kasar.
(RFI)
No comments