An Cafke Mahaifin Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Jariri Bayan Ya Karbi Haihuwarsa Ta Youtube



Daga Umar Shuaibu

An kama wani mutum a kasar Indiya bayan da ya yi sanadiyyar mutuwar jaririn da matarsa ta haifa. 

R. Loganathan mai shekaru 34 daga Tamil Nadu, da matarsa L. Gomathi suna sa ran samun jaririn a ranar 13 ga watan Disamba, amma an samu jinkiri sai ranar 18 ga watan Disamba matar ta fara nakuda.

Loganathan ya nemi taimakon 'yar uwarsa Geetha, kuma ya yi Æ™oÆ™arin karbar haihuwar matar ta shi tare da taimakon wasu bidiyon koyarwa a YouTube. A dalilin haka jaririn ya rasu yayin haihuwar, ita kuma mahaifiyar jaririn ta rasa jini mai yawa. 

An kwantar da matar a Cibiyar Kula da Lafiya a matakin Farko ta Punnai cikin mawuyacin hali, jim kadan bayan haka aka maida ita zuwa Asibitin Kwalejin Kiwon Lafiya ta gwamnati da ke Vellore. 

"Za a dauki tsauraran matakai kan irin wadannan ayyuka da ke jefa rayuwar uwa da jariri cikin haɗari. Kuma za a ƙara fadakar da al'umma dangane da haihuwa cikin sauki a asibiti." Inji D. Bhaskara Pandian, Jami'in da ke kula da Gundumar Ranipet.

Post a Comment

0 Comments