Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Ci Galabar Ebola A Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo

Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo ta ce, a hukumance an kawo karshen cutar Ebola wadda ta barke a baya-bayan nan a kasar, inda aka ...


Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo ta ce, a hukumance an kawo karshen cutar Ebola wadda ta barke a baya-bayan nan a kasar, inda aka shafe tsawon kwanaki 42 ba tare da samun mutun ko guda  dauke da cutar ba.

A ranar 8 ga watan Oktoban da ya gabata ne, aka tabbatar da sake bullar cutar ta Ebola bayan ta kashe wani yaro dan shekara uku a wancan lokacin a garin Beni da ke lardin arewacin Kivu a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyar Congo.

Daga bisani hukumomin kasar sun sake tabbatar da mutane 8 da cutar da kara kamawa, yayin da aka samu mutane 9 kuma da suka mutu a  garin na Beni cikin watanni biyu.

Ministan Kiwon Lafiyar Congo, Jean Jacques Mbungani ya ce, an samu jinkirin gano sake barekwar cutar ta Ebola saboda yajin aikin da ma’aikatan kiwon lafiya suka shiga  a wancan lokaci.

Sai dai a jiya Alhamis Ministan ya fito karara ya shaida wa duniya cewa, sun kawo karshen wannan annoba a hukumance bayan sun dauki kwanaki 42 suna sanya ido ba tare da gano ko mutun guda ba sabon kamuwa da cutar.

Daga cikin matakan da hukumomin kasar suka dauka na yaki da cutar, har da allurra rigakafin da aka tsikara wa jama’a da dama jim kadan da sake bullarta.

No comments