Hoto: Stephenie Rodriguez tare da kafafuwa na roba da aka sa mata Abin mamaki ba ya karewa a duniya. Wata Baturiya '...
Hoto: Stephenie Rodriguez tare da kafafuwa na roba da aka sa mata
Abin mamaki ba ya karewa a duniya. Wata Baturiya 'yar kasar Austaraliya mai suna Stephenie Rodriguez ta bayyana wasu hotunanta da ta ce an yanke mata kafafuwa biyu saboda matsalolin rashin lafiyar da ta samu bayan sauro ya cije ta a Nijeriya.
Mujallar Good Weekend ta Austaraliya ita ta bayyana wannan labari na Stephenie, wacce sauro ya cije ta a 2019, kuma ya kwantar da ita a asibiti, inda ta yi ta kokarin ceto ranta.
A sanadiyyar cizon sauron Nijeriya, sai da aka yi mata dinki 36 a jikinta, karshe kuma aka guntule kafafuwan ta biyu aka sa mata na roba.
Kamar yadda rahoton ya ce, Stephenie ita ce mace ta farko a Austaraliya da aka guntule wa kafafuwa biyu tun daga gwiwa aka sa mata na roba.
To, jama'a sai ku kara gode wa Allah da ya sa ku kwana kuke ku tashi da sauron Nijeriya, amma lalurar da hakan ke haifarwa bai kai na wannan mata ba.
No comments