Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Hana Yin Dariya Tsawon Kwanaki 11 A Koriya Ta Arewa

Hausawa dai su ka ce "Allah ɗaya, gari bamban". Yayin da likitoci ke kira da a riƙa yin murmushi da dariya domin gujew...


Hausawa dai su ka ce "Allah ɗaya, gari bamban". Yayin da likitoci ke kira da a riƙa yin murmushi da dariya domin gujewa kamuwa da ciwon hawan jini da damuwa, Ita kuwa Gwamnatin kasar Koriya Ta Arewa hana dariyar ta yi. Duk wanda a ka ga fuskarsa akwai alamar farin ciki, to kuwa zai ɗanɗana kuɗarsa a ƙasar.

Gwamnatin kasar ta saka wannan zazzafar dokar ne domin yin jimamin cika shekaru 10 da  rasuwar shugaban ƙasar, Kim Jong-il.

Jaridar The Telegraph ta ruwaito cewa an kuma hana yin dariya da shan barasa har tsawon kwanaki 11 na jimamin tunawa da rasuwar tsohon shugaban ƙasar.

Yau 17 ga watan Disamba, shi ne daidai shekaru 10 da rasuwar Kim Jong-il, kuma da ga yau za a hana ƴan kasar zuwa yin sayayya a kantuna.

"A lokacin yin jimamin, an hana mu yin dariya, shan giya ko kuma yin wasu abubuwa na farin ciki," in ji wani ɗan kasar da ke Arewa-maso-Gabas da bodar Sinuiju yayin da ya ke shaidawa gidan rediyon Radio Free Asia (RFA).

"Ko da ma wani ya rasu a dangi a cikin kwanakin jimamin,  to ba wanda ya isa ya yi kuka a bayyane kuma ba za a binne gawar ba sai bayan kawanakin jimamin. Idan kuwa ranar haihuwar mutum ta faɗo cikin kwanakin jimamin, to fa sai dai a hakura don ba za a yi bikin zagayowar ranar haihuwa ba," in ji shi.

Kim Jong-il, wanda ya mulki ƙasar da ga shekarar 1994 zuwa shekarar 2011 lokacin da ya rasu sakamakon ciwon zuciya, shi ne mahaifin Shugaban Ƙasar na yanzu, Kim Jong-un.

Kim Jong-il ya mulki ƙasar tsawon shekaru 17 kafin rasuwarsa a shekarar 2011.

No comments