Wakilin MADOGARA TV/Radio a Katsina, Zaharaddeen Sirajo Abbas na karbar girmamawar a yayin taron. A ranar Litinin din...
Wakilin MADOGARA TV/Radio a Katsina, Zaharaddeen Sirajo Abbas na karbar girmamawar a yayin taron.
A ranar Litinin din da ta gabata ne aka gudanar da bikin Katsina Facebook Connect a dakin taro na Minaj's Event Center da ke cikin Birnin Katsina. Bikin wanda ya hada manyan manyan mutane tun daga Gwamnan jihar Rt. Hon. Alhaji Aminu Bello Masari, 'yan Majalisar Tarayya, 'yan Majalisar jiha, Malaman addini, masu Sarautar Gargajiya, Malaman Jami'o'i, 'yan kasuwa, manya da kanana tare da jami'an tsaro da kuma samari da 'yan mata.
An fara gudanar da taron kamar yadda aka tsara da misalin karfe 10 na safe, inda Alhaji Abba Yusufu ya fara da maraba da baki daga bisani kuma Alhaji Al'ameen Isah, shugaban Kafafen sadarwa na zamani kuma mai bai wa Gwamna shawara ya gabatar da takaitaccen jawabi, sai kuma Honorabul Abduljalal Haruna Runka ya gudanar da jawabi a madadin Majalisar Dokokin jihar Katsina.
Nishadantarwa daga wata zazzakar matashiya daga Kano mai suna Rahma Adam Kano. Sai tattaunawa kashi na daya akan rawar da kafafen sadarwa na zamani ke takawa wajen inganta tsaro, bunkasa tattalin arziki, da kuma ci gaban al'umma.
Jagoran tattaunawar shi ne Mustapha S Umar, mai tattauna Barista MS. Mahuta, Kwamishinan jihar katsina, AS sucurity Malam lbraheem Katsina sai na karshe matashin dan siyasa Abduljabar Sirajo Guga.
Jawabin Gwamnan jihar Katsina RT Honorabul Aminu Bello Masari ya fara da bada hakuri kasantuwar rashin halartarsa cikin lokaci, ya ci gaba da nuna murnarsa akan kokarin shirya taron. Ya ja hankalin matasa akan dogaro da kai, inda ya ce ya san matasan jihar Katsina suna da kokari da hazaka duk inda ka dauki matashin Katsina ka saka shi wallahi ko lalata ake ba za a barshi baya ba.
Daga karshe an kaddamar da Mujalla wacce aka shirya domin taron, inda aka kira Rt Hon Abubakar Yahya Kusada ya gabatar da ita, daga bisani aka kirawo manyan kafafen watsa labarai din da suka zo wurin aka girmama su da ita ciki kuwa har da MADOGARA TV/RADIO, Katsina Post, FuntuwaTV, HKTv, Liberty da Aminiya.
A na shi bangaren shugaba kuma wanda ya kirkiro wannan taro wanda aka gudanar da kashi na biyu, Malam Muhammad Aminu Kabir ya fara da godiyar ga Allah ganin yadda aka gudanar da taron cikin nasara, ya kuma kara da cewa ya kamata matasa mu yi amfani da kafar wajen yin abubuwan da suka dace maimakon na Allah wadai daga karshe ya yi addu'a Allah ya mai da kowa gidansa lafiya.
No comments