Kungiyar dake kare hakkokin ‘Yan Jaridu a duniya ta CPJ ta ce adadin ‘Yan Jaridun da aka tsare a shekarar 2021 ya zarce yadda ak...
Kungiyar dake kare hakkokin ‘Yan Jaridu a duniya ta CPJ ta ce adadin ‘Yan Jaridun da aka tsare a shekarar 2021 ya zarce yadda aka saba gani a shekarun baya, lura da cewar ‘Yan Jaridu 293 aka garkame a gidajen yari a wannan shekarar, yayin da aka kashe wasu 24.
Rahotan da kungiyar CPJ ta fitar na wannan shekarar ya ce daga cikin ‘Yan Jaridu 293 da aka tsare a gidan yari bana, kasar Chana ke sahun gaba wajen garkame manema labaran da yawan su ya kai 50, sai Myanmar mai 26 a matsayin na kasa ta 2 sannan Masar a matsayi na 3 da ‘Yan Jaridu 25.
Sauran kasashen dake cikin 10 na farko sun hada da Vietnam da Belarus da Turkiya da Eritrea da Saudi Arabia da Rasha da kuma Iran.
Daraktan kungiyar Joel Simon ya danganta matsalolin da ake samu wadanda suke kai wa ga garkame ‘yan Jaridun a gidan yari da suka hada da kokarin wasu gwamnatoci na mamaye kafofin yada labarai da kuma sanya ido akan yadda ake gudanar da aikin jaridar.
Simon ya ce daure ‘yan Jaridu saboda yadda suke gudanar da aikin su wata alama ce ta nuna yadda gwamnatin kama karya ke aiki.
CPJ ta kuma ce har yanzu ana ci gaba da kai wa ‘Yan Jaridun hari ana kuma kashe su, kamar yadda aka gani a wannan shekara mai karewa a wasu kasashe, inda aka hallaka ‘yan Jaridu 24.
Daga cikin kasashen da ake yi wa manema labaran kisan gilla kuwa, India ke sahun gaba da ‘Yan Jaridu 4 sai kuma Mexico mai ‘Yan Jaridu guda 3.
No comments