Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

AN KUMA: Kotun Abuja Ta Amince Da Zaben Bangaren Shekarau A Kano

Wata Kotu a Abuja ta tabbatar da shugabancin Alhaji Ahmadu Danzago a matsayin shugaban Jam’iyyar APC dake Jihar Kano saboda yadd...


Wata Kotu a Abuja ta tabbatar da shugabancin Alhaji Ahmadu Danzago a matsayin shugaban Jam’iyyar APC dake Jihar Kano saboda yadda ta gudanar da tarurrukan Jam’iyyar a matakan mazabu da kananan hukumomi da kuma Jiha.

Mai shari’a Hamza Mua’zu ya amince da bangaren Malam Ibrahim Shekarau kamar yadda ya shigar da kara a gaban sa inda yake kalubalantar bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da shugaban bangaren sa Abdullahi Abbas dake ikrarin gudanar da halartaccen zabe.

Alkalin kotun yayi watsi da bukatar bangaren Gwamna Ganduje na dakatar da shari’ar, yayin da ya umurce su da su biya tarar naira miliyan guda saboda abinda ya kira bata lokacin kotu.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau © Shekarau

Kotu ta amince da tarurrukan da bangaren Malam Shekarau ya gudanar wanda ya tabbatar musu da shugabancin Jam’iyyar a Jihar Kano.

Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta fada rikicin cikin gida a tsakanin ‘yayan ta lokacin gudanar da tarurrukan zaben shugabanni a matakai daban daban, abinda ya kaiga samun bangarori guda biyu da suka hada da na tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau da kuma na Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje.

Wannan ya kaiga gudanar da tarurrukan jam‘iyyar guda biyu da kuma samun shugabannin bibbiyu a matakai daban daban na jihar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewar 'Dan Majalisar Tarayya dake wakiltar Jihar Kano Sha’aban Sharada ya dauki nauyin shari'ar da kuma tarurrukan bangaren jam'iyyar dake kalubalantar Gwamna Ganduje.

A bangare guda Gwamna Abdullahi Ganduje ya bukaci 'yayan jam'iyyar APC a Jiahr da su kwantar da hankalin su dangane da wannan hukunci, inda yace suna ci gaba da nazari akan sa.

Wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Mohammed Garba ya rabawa manema labarai yace tunda rikici ne na cikin gida, gwamnati da APC na nazari domin dubar mataki na gaba da za'a dauka.

(-RFI)


No comments