Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Lamuncewa Jami'ar MAAUN Ta Fara Karatun Lauya A Matakin Digiri

Daga Ali Kakaki Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) na sanar da jama’a cewa Hukumar...


Daga Ali Kakaki

Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) na sanar da jama’a cewa Hukumar lura da Jami’o'in kasa (NUC) ta bai wa jami’ar izinin ba da digiri a bangaren karatun Lauya (LLB) a shirye-shiryen karatunta na digiri. 

Hakan na kumshe ne a cikin wata sanarwa da shugaba kuma wanda ya kafa jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya rabawa manema labarai a Kano a ranar Alhamis.

A cewar sanarwar, daliban da ke son karantar nazarin huldar kasa da kasa (International Relations) za su iya ci gaba da neman darasin saboda babu wani abin damuwa ko firgici.

A cewar sanarwar, jami’ar za ta kuma fara karatu da wasu kwalejoji uku.

Sai dai kuma ya bayyana cewa maki 120 kawai ake bukata daga jarabawar JAMB. 

Kwalejojin sune kamar haka; 

A. Kwalejin Kwamfuta da lura da bayanai (College of Computer and Information management). 

A karkashi akwai darussa kamar haka; 

1. BSc  Computer Science. 
2. BSc Cyber Security.
3 .BSc Software Engineering.
4 .BSc Information Technology.

B. Kwalejin Gudanarwa da Kimiyyar zamantakewa (College of Management and Social Science). 

1. BSc Accounting.
2. BSc Human Resources Management.
3. BSc Business Administration.
4. BSc Economics.
5. BSc Banking and Finance.
6. BSc Mass Communication.
7 .BSc International Relation.
8. BSc Peace Studies and Conflict Resolutions.

C.  Kwalejin Kimiyyar Lafiya (College of Medical Sciences).

1. BNSc Nursing Science.
2. BMLS  Medical Laboratory Sciences.
3. B.Physiotherapy.

D. Makarantar Shari'a (School of Law).

1. Bachelor of Law 

No comments