Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Nada Farfesa Gwarzo Wazirin Hausawan Turai

Daga Ali Kakaki   A jiya Asabar 4 ga watan Disambar 2021, Mai Martaba Hausawan Turai, Alhaji Sirajo Jan Kado ya daga darajar S...


Daga Ali Kakaki 

A jiya Asabar 4 ga watan Disambar 2021, Mai Martaba Hausawan Turai, Alhaji Sirajo Jan Kado ya daga darajar Sarautar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo daga Sardaunan Hausawan Turai zuwa Wazirin Hausawan Turai. 

Bukin nadin sarautar sabon Wazirin wanda aka gudanar da shi a fadar Hausawan Turai dake birnin Paris babban birnin kasar Faransa ya samu halartar dimbin masoya sabon Wazirin Hausawan na Turai sannan kuma tsohon Sardaunan Hausawan Turai. Taron ya yi armashi kwarai da gaske. 

Da yake jawabi ga mahalarta taron a yayin nadin a madadin Sarkin Hausawan, Santurakin Turai, Alhaji Aminu Fanda ya bayyana cewa  masarautar na Hausawan Turai ta yanke shawarar daga darajar sarautar Farfesa Gwarzo ne saboda yadda yake dawainiyya da masarautar da 'ya'yanta da sauran al'ummah a fadin duniya baki daya. 



Santurakin ya kara bayyana wa mahalarta taron bukin nadin sarautar cewa, a matsayin Farfesa Adamu Gwarzo na shahararen dan jarida wanda har ya taba rike shugaban kungiyar kare hakkin 'yan jarida na Afrika sau biyu, yanzu haka kuma shi ne mamallakin  Rukunin jami’o'in Maryam Abacha American University dake Nijer da Nijeriya sannan kuma da Jami'ar Franco-British University dake Kaduna a Nijeriya. Kazalika kuma shi ne shugaban kungiyar jami’o'in Afrika masu zaman kansu.  

Wazirin Hausawan Turai, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya godewa Allah (SAW) da ya ba shi rai da lafiya da kuma ikon taimakon al'ummah ba tare da wani gajiyawa ba, sannan ya godewa Hausawan Turai da 'yan majalisar Masarautar da suka daga darajar sarautarsa daga Sardauna zuwa Waziri. 

Shugaban rukunin jami’o'in ta Maryam Abacha American University dake Nijer da Nijeriya ya kuma godewa wadanda suka halarci taron bukin daga darajar sarautarsa zuwa Waziri; "haka kuma ina kara mika godiya ta musamman ga dimbin masoya da suka rika kiranmu ta wayar GSM suna taya ni murna da farin ciki da kuma wadanda suka rika aiko mun da sakon taya murnar su ta hanyonyin kafafen sada zumunta. Nagode! Nagode! Nagode Allah (T) ya saka muku da alherinsa sannan ya kara dankon zumuncin dake tsakanina da ku ya ku jama'a."

No comments