Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'An Sallamawa 'Yan Ta'adda Yankin Shinkafi Ta Jihar Zamfara'

Daga Ahmad Mathscom Turji da tawagassa sun datse hanyar shiga kasuwar Shinkafi daga Kaura zuwa Shinkafi da kuma daga Isa zuwa Sh...


Daga Ahmad Mathscom

Turji da tawagassa sun datse hanyar shiga kasuwar Shinkafi daga Kaura zuwa Shinkafi da kuma daga Isa zuwa Shinkafi tun karfe bakwai (7:00am) na safiyar Alhamis har zuwa karfe goma (10:00pm) na daren Alhamis, sun kona motoci tare da sace mutane a ranar ba tare da wani daga mahukumtan jihar Zamfara ko shugabancin kasa sun dau wani mataki ba.

Wani abin al'ajabi shi ne yadda wannan hare-haren ya dauki tsawon lokaci yana gudana kai ka ce TURJI ne yake shugabantar yankin, domin  babu wani jami'an tsaro ko daya da ya kawo dauki a wannan yankin. 

Hankali yana iya yadda da sallamawa rundunar Turji wannan yanki aka yi domin cimma bukatun siyasa. 

Ana kashe al'umma a yankinmu kai ka ce babu hisabi a kiyama da Ubangiji zai yi tsakanin mahukumta da al'ummar  wannan yanki na mu. Ko kuwa sun zabi duniya ce sun kyale lahira.

Allah zai yi shari'a tsakaninmu da ku akan jinainan 'yan'uwanmu da aka shekar ba tare da hakkin shari'a ba.

Wallahi bamu yafe ba, Allah ya gaggauta kawo mana mummunar karshen ku cikin kaskanci da tozarta. 

No comments