Hukumar Ƴan sandan Farin Kaya, SSS ta shawarci ƴan majalisar tarayya da na jihohi, sanannun mutane, matafiya da ɗalibai da su k...
Hukumar Ƴan sandan Farin Kaya, SSS ta shawarci ƴan majalisar tarayya da na jihohi, sanannun mutane, matafiya da ɗalibai da su ka zo hutu da su kiyaye su ka guji wuraren da ɓatagari za su iya illata su.
Dakta Peter Afunanya, kakakin hukumar SSS ne ya bada wannan shawarar a taron manema labarai a yau Talata a Abuja.
Ya kuma gargaɗi masu ɗaukar nauyin garkuwa da mutane, fashin daji, ta'addanci, da sauran laifuka da su gaggauta daina wa.
"Bari na sake nanata wa cewa duk waɗanda su ke ɗaukar nauyin garkuwa da mutane fashin daji, ta'addanci, da sauran laifuka da su gaggauta canja tunani.
"Su masu aikata waɗannan laifukan, ko a Arewa ko a Kudu, sun san kansu. Babu tantama cewa tura ta kai bango, sabo da haka yanzu lokaci ya yi da za a sanya ƙafar wando ɗaya da su,"
Afunanya ya yi kira ga iyaye da su sanya idanu a kan ƴaƴan su yayin da su ke dawowa hutun Kirsimeti.
Ya kuma yi kira ga malamai da sarakunan gargajiya da su kame harsunan su daga munanan maganganu, in da ya ja kunnen su game da yin kalaman tunzuri.
No comments