An Yi Wa Ƴan Sanda Ƙarin Albashi A Nijeriya


Gwamnatin Najeriya ta amince da ƙarin kashi 20 na albashin ƴan sanda.

Ministan ma’aikatar kula da harakokin ƴan sanda Muhammad Dingyadi wanda ya tabbatar da matakin ga manema labarai bayan taron majalisar ministoci da shugaban Buhari ya jagoranta ya ce ƙarin zai fara aiki ne daga watan Janairu, kamar yadda Jaridar The Punch ta ruwaito.

Ya ce an amince da ƙarin ne domin ƙarfafa guiwar ƴan sanda a sassan ƙasar.

Post a Comment

0 Comments