Mahukuntan Jamus za su takaita wasu harkoki na walwalar wadanda ba su yi allurar rigakafi ba, a yankunan da asibitoci ke cika da...
Mahukuntan Jamus za su takaita wasu harkoki na walwalar wadanda ba su yi allurar rigakafi ba, a yankunan da asibitoci ke cika da masu corona.
DW ta labarto cewa; shugabanni na tarayya da jihohin kasar 16, a wani taron da suka gudanar a ranar Alhamis suka cimma wannan matsaya na ba-sani-ba- sabo, wanda ke zama martani ga barazanar sake ta'azzarar cutar corona a karo na hudu a Jamus.
Daga yanzu sai wanda ke da shaidar yin allura ko kuma bai jima da warkewa daga cutar ba ne, zai iya shiga wuraren wasanni ko cin abinci da makamantansu a yankuna da cutar ta fi kamari.
Saxony, ita ce jihar da ta fi kowacce shiga cikin wadi-na-tsaka-mai wuya na yaduwar cutar coronar a karo na hudu, tuni kuma ta fara la'akari da kafa dokar kulle tare da rufe mafi yawan wuraren shakatawa.
Jihar ce dai aka fi samun karancin masu allurar rigakafi a yankin gabashin Jamus, kuma ke da mafi yawan wadanda suka kamu da COVID 19 a cewar rahoton.
No comments