Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ayyukan Buhari Da Gwamnoni Na Nuna Cewa Rayukan Talakawa Ba Su Da Daraja - ACF

Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce ayyukan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da gwamnonin yankin arewacin...


Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce ayyukan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da gwamnonin yankin arewacin ƙasar game da kashe-kashen 'yan fashi a fakaice na nuna cewa "rayuwarsu ce da ta iyalansu ce kaɗai ke da daraja".

Ƙaungiyar ta yi kira ga shugaban da gwamnonin da su "tausaya" wa mutanen da hare-haren 'yan fashin daji suka shafa ta hanyar ziyartar wuraren.

"ACF na nuna rashin jin daɗinta game da abin da ya zama kamar wata liyafar kisa maras ƙarshe da ke faruwa a arewacin Najeriya," a cewar sanarwar da sakataren ƙungiyar Emmanuel Yawe ya sanya wa hannu.

"Yayin da ACF ke bin sahun gwamnan Kaduna da shugaban ƙasa wajen yin alhinin waɗanda suka rasu, muna kuma kira ga dukkan gwamnatocin jiha da ta tarayya da su nuna ƙarin tausayi a irin wannan matsala ta rashin tsaro.

"Babu abin da zai hana shugaban ƙasa ko gwamnan jiha ziyartar irin waɗannan wurare. Mun lura cewa bai (Buhari) taɓa tunanin cewa ya kamata ya je ba. Hasali ma saboda koyi da suke yi shi, babu wani gwamna da ya yi hakan sai Babagana Zulum na Borno.

"Ayyukan shugban ƙasa da gwamnonin Arewa a fakaice na nuna cewa rayukansu ne kaɗai da na iyalansu ke da daraja."

Sanarwar ta ƙara da cewa "ACF ta yi imanin cewa shugaban ƙasa da gwamnonin Arewa na da damar da za su gyara".


-BBC Hausa

No comments