Ministan yaÉ—a labaran Nijeriya Alhaji Lai Mohammed ya ce ba don zuwan Shugaba Buhari ba da matsalar tsaron Nijeriya ta fi muni. A wani tar...
Ministan yaÉ—a labaran Nijeriya Alhaji Lai Mohammed ya ce ba don zuwan Shugaba Buhari ba da matsalar tsaron Nijeriya ta fi muni.
A wani taron manema labarai a Abuja, Lai Mohammed ya ce Buhari ya mayar da batun tsaro a matsayin babban ginshikin gwamnatinsa kamar yadda BBC ta labarto.
Ya ce magance matsalar tsaro na É—aya daga cikin ubu uku da gwamnatin APC ta fi ba fifiko.
"Buhari ya samar da ingantaccen shugabanci domin zaburar da jami'an tsaro wajen magance matsalar tsaro."
"Babu wata gwamnati a Nijeriya a baya-bayan nan da ta samar wa jami'an tsaro abubuwan da suke buƙata kamar ta Shugaba Buhari," in ji ministan.
Ministan dai na mayar da martani ne ga masu ganin sha'anin tsaro ya ƙara taɓarɓarewa zamanin gwamnatin APC ta Buhari.
Lai
Mohammed ya ce "tsokaci da siyasantar da yanayin tsaron ƙasa da ake yi
inda wasu ke bayyana damuwa wasu kuma sun mayar da batun siyasa."
Ministan
duk da ya ce yanayin tsaron da ake ciki na ci gaba da zama babban ƙalubale,
kuma wasu sun damu amma akwai waÉ—anda ya ce suna son amfani da damar don
buƙatun kansu.
"Idan
aka dubi abin da ke faruwa a yanzu, ba tare da tunanin yadda matsalar za ta
ƙazance ba, ba don shugaba Buhari ya ɗauki matakai ba kan abin da ya shafi
halin tsaro da matsalar ta fi muni."
A
cewar Lai Mohammed ba don Buhari ba da Boko Haram ta ayyana kafa Daular Islama
a Najeriya, yana mai cewa a 2014 Boko Haram ta kafa Daula a Gwoza bayan kama
Bama da Gamboru da wasu garuruwa na jihohin Borno da Yobe da Adamawa tare da
dora sarakunansu da ke ƙarbar haraji kafin sojojin Najeriya suka tarwatsa su.
Sai
dai ministan ya yarda cewa matsalar tsaron Nijeriya ta ƙara muni sakamakon
matsalar ƴan bindiga ɓarayin daji masu satar mutane.
Amma
ya jaddada cewa "Shugaba Buhari ya yi ƙoƙari duk da ana cikin yanayi na taɓarɓarewar
tattalin arziki wajen tunkarar matsalolin tsaron ƙasa kuma zai ci gaba da
ƙoƙari domin kare rayukan ƴan Nijeriya."
"Ga
masu cewa Buhari ya gaza ba gaskiya ba ne, kawai siyasa ce.
"Yadda
ya ƙara yawan jami'an tsaro, shugaban ya saita su yadda za su magance matsalar
tsaro ba wai kawai zamanin mulkinsa ba har zuwa bayan ya sauka," in
ministan.
No comments