Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi watsi da duk alkawuran da ta yi ba lokacin yakin neman zaɓe kafin ...
Shugaban
kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi watsi da duk
alkawuran da ta yi ba lokacin yakin neman zaɓe kafin cikar wa’adinsa.
Shugaban
ya bayyana haka ne a sakonsa na Kirsimeti ga ’yan Nijeriya, inda ya ce yana
taya Kiristoci a Najeriya farin ciki kamar sauran mabiya a duniya don gudanar
da bikin a wannan shekarar.
A cikin
saƙon, shugaban ya roƙi ƴan Nijeriya su yi rigakafin korona domin rage bazuwar
annobar.
Ya kuma
taɓo batun tsaro inda ya ce duk da nasarorin da jami’an tsaro suka samu amma
har yanzu akwai ƙalubale.
“Ina
kira ga ƴan Najeriya da su yi imani da mu da kuma ɗaukar abubuwan da ke faruwa
a matsayin wani lokaci da kuma zai wuce, kamar sauran yanayi marar daɗi a
tarihin ƙasar.”
“Wannan
gwamnatin ba za ta yi watsi da alƙawullan da ta yi wa ƴan Nijeriya ba,” in ji
shugaban.
Tushe: BBC
No comments