Shugabannin gudanarwar Jam’iyyar PDP a Nijeriya, sun yi watsi da zargin cewar wasu daga cikin su sun karbi kudade daga Gwamnan J...
Shugabannin gudanarwar Jam’iyyar PDP a Nijeriya, sun yi watsi da zargin cewar wasu daga cikin su sun karbi kudade daga Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki kafin bashi tikitin takarar zaben shekarar 2020.
Sakataren yada labaran Jam’iyyar Kola Ologbodian ya yi watsi da wannan zargi, inda ya bukaci gwamnan da ya fito fili ya bayyanawa duniya wadanda suka karbi kudi a hannunsa domin a san su, maimakon bata musu suna baki daya.
Ologbodian ya ce babu wani ‘dan majalisar gudanarwar jam’iyyar guda da ya karbi kudi daga hannun gwamnan a matsayin cin hanci, saboda haka suna bukatarsa da ya bayyana matakan da aka bi wajen ba shi tikitin da kuma kudin da ya biya.
Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike na daga cikin wadanda suka dade suna zargin shugabannin jam’iyar ta su da almundahana wajen tsayar da Obaseki da mataimakinsa Philip Shuaibu.
Wike ya bayyana shugabannin a matsayin masu karbar haraji, inda ya yi barazanar gabatar da shaidu akan su muddin suka kalubalance shi.
Ologbodian ya ce a karkashin jagorancin su sun yi iya bakin kokarin su wajen lashe kujerun gwamnoni 17 a zaben shekarar 2019 kafin Jam’iyyar APC ta kwace Jihar Imo, yayin da wasu gwamnonin PDPn 3 kuma suka sauya sheka.
Jam’iyyar PDP ta zabi Farfesa Iyorchia Ayu a matsayin sabon shugaban ta domin maye gurbin Uche Secondus da aka dakatar kafin karewar wa’adin mulkinsa.
No comments