Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Barrow Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Gambia

Hukumar Zabe a kasar Gambia ta bayyana shugaba Adama Barrow a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a karshen m...


Hukumar Zabe a kasar Gambia ta bayyana shugaba Adama Barrow a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a karshen mako, sakamakon lashe kashi 53 na kuri’un da aka kada, yayin da Ousainou Darboe ya zo na biyu da kashi 28 kamar yadda gidan Rediyon Faransa ya labarto. 

Shugaban hukumar zaben Alieu Momarr Njai ya gabatar da sakamakon zaben wanda ya bayyana shugaba Adama Barrow a matsayin wanda ya lashe, sa’oi kadan bayan wasu daga cikin 'yan takarar sun kalubalanci sakamakon cikin su harda Darboe.

Zaben wanda shi ne irin sa na farko tun bayan kawar da tsohon shugaban kasa Yahya Jammeh daga karagar mulki, ya zama wani zakaran gwajin dafi ga jama’ar Gambia.

Shugaban tawagar sa ido na kungiyar ECOWAS, Ernest Bai Karoma ya roki 'yan takarar da su amince da sakamakon zaben kafin gabatar da shi.

Tuni magoya bayan Barrow suka fara bukukuwan samun nasara a birnin Banjul.

Idan dai ba a manta ba, Barrow ne ya kada shugaba mai-ci Yahya Jammeh shekaru 5 da suka gabata, abin da ya kawo karshen mulkinsa na shekaru 22, ya tilasta masa barin kasar domin samun mafaka a kasar waje. 

No comments