Adam Umar Omajido shi ne shugaban rundunar shiyya na 'Police Neighborhood Watch' dake garin Tafa na karamar hukumar Kaga...
Adam Umar Omajido shi ne shugaban rundunar shiyya na 'Police Neighborhood Watch' dake garin Tafa na karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.
Omajido ya koka ne da dabi'un wasu batagarin jami'an tsaro a kasa baki daya.
Shugaban na 'Neighborhood Watch' dake Tafa dake karamar Hukumar Kagarko, ta jihar Kaduna ya nuna damuwarsa ne a daidai lokacin da jama'a ke kushe gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari sakamakon zanga-zangar da ta barke a wasu jihohin Arewa dake nuna damuwar jama'ar Arewa akan kisan kiyashi da ake yi wa jama'a ba ji ba gani dare da rana.
Bisa haka ne shugaban shiyyar ya ce, a gaskiya idan anga laifin bera to dole a ga ta Daddawa a don haka ko da akwai laifin gwamnati to akwai laifin batagarin cikinta wato masu fitar da sirrin jami'an tsaro na gaskiya.
Shugaban ya ce da yawan lokaci gwamnati tana bakin kokarinta amma batagarin suke rugaza dukkan shirin da gwamnati ke gudanarwa wanda hakan kansa maharan samun nasara a kan jami'an tsaron na gaskiya.
Don haka ne ya ce, dole ne gwamnati ta canza salon yaki. Ya ce daga ciki abin da za su kawowa dukkan jami'an tsaron tun daga kasa har sama shi ne a rika aikin tsaro don Allah ba don tare abin duniya ba.
Kuma ya yi kira da yin adalci a yayin hukunci wato ba sani ba sabo. Ya ce babban abin kunya ne a cikin wannan yanayi sai ka ga an kama jami'in tsaro da hannu dumu-dumu a wajalen taimakawa 'yan ta'adda, ya ce hakan cin amanar kasa ne kai tsaye.
Ya ce wajibi ne duk wani jami'in tsaro ya sani an dauke shi ne karkashin doka da Oda don haka hakuri ne ke maganin komai hakuri da albashi da ake baka shi zai sanya ka sami natsuwa a wajen aikin ka ba sai ka hada baki da barawo ko Dan fashi ba.
Da shugaban ya juya kan gwamnati kuwa kira ya yi ga gwamnati cewa, dole in ana son kawo karshen 'yan ta'adda to sai an rika duba wanda suke yin aikin don Allah masu nuna kishin kasa.
Ya ce kula da hakkin jami'in tsaro na kara mishi kwarin guiwa da kwarjini yayin aikinsa. Ya kuma ja hankalin dukkan jami'an tsaro ko wani iri ne da su ji tsoron Allah yayin gudanar da aikinsu hakan ya ce zai ba su kariya a wajen gudanar da aikinsu.
Shugaban tuni ya bayyana wani nasara da kungiyar ta su ta samu na damke daya daga cikin masu garkuwa da mutane kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a 'yan kwanakin nan.
Ya ce nasarar ta biyo baya ne sakamakon dagewa da 'ya'yan kungiya ta su ke yi dare da rana.
Ya kuma roki gwamnati da ta kawo masu taimakon gaggawa domin karawa hanyar ta Abuja zuwa Kaduna kariya mai inganci.
Ya ce rashin samun motoci da tallafi da gwamnati ta saba ga jami'an tsaro irinsu wanda duk wahala basa gudummawa ga 'yan ta'adda yana kawo masu tsaiko matuka.
Don haka ne ya yi fatan masu fada aji na hukumomin tsaro za su ankare da gudummawar wannan kungiya ta 'Police Neighborhood Watch' dake da ofishinta a garin Tafa dake karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.
Ya ce kungiyarsu tana aiki da rundunar 'yan sanda kafada da kafada wanda hakan yasa ake samun saukin ta'addanci a kan hanyar ta Abuja a halin yanzu.
Tabbasa bincike ya nuna cewa kungiyar ta su tana taka rawar gani a bangaren tsaro akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Kuma tabbas rashin abin hawa na daga cikin abin dake kawowa kungiyar cikas amma ba ma'aikata ba.
Allaah ya shiga al'amarin.
ReplyDelete