Wata kotu a Jamhuriyar Nijar ta ba da damar gudanar da zanga-zangar da kungiyoyin farar hula suka shirya gudanarwa a yau Lahadi ...
Wata kotu a Jamhuriyar Nijar ta ba da damar gudanar da zanga-zangar da kungiyoyin farar hula suka shirya gudanarwa a yau Lahadi domin neman rufe sansanonin sojojin kasashen waje da ke kasar.
Daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar Maikoul Zodi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kotu ta yanke hukuncin ne a ranar Juma’a, inda kuma ta bukaci 'yan sanda su kula da gudanar zanga-zangar cikin lumana.
A cewar Zodi sun bukaci yin zanga-zangar kan neman ficewar dukkan sansanonin sojojin kasashen waje musamman na Faransa, saboda yadda suka shafe shekaru takwas suna Nijar ba tare da kawo karshen matsalolin tsaron da suke fuskanta ba.
A karshen watan Nuwamba, ayarin motocin sojojin Faransa dake kan hanyarsu ta zuwa kasar Mali suka fuskanci turjiya a garin Tera dake jamhuriyar Nijar bayan shafe sama da mako guda ana gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da jerin gwanon motocinsu a Burkina Faso. Inda daga karshe sojojin Faransa suka budewa masu zanga-zangar wuta suka kashe da dama tare da jikkata da dama kamar yadda majiyarmu ta tabbatar.
No comments