Daga Umar Shuaibu A ranar Juma'a 24 ga watan Disamba 2021, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Injiniya Mu'azu ...
Daga Umar Shuaibu
A ranar Juma'a 24 ga watan Disamba 2021, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Injiniya Mu'azu Sambo a matsayin Minista.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da taron ne jim kadan gabanin bude taron kwamitin tsaro na kasa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
NAN ta ruwaito cewa Sambo, wanda ya maye gurbin tsohon ministan wutar lantarki, Mamman Sale, daga Jihar Taraba, an mayar da shi ma’aikatar ayyuka da gidaje a matsayin ministan ayyuka da gidaje.
No comments