Akalla mutane 101 suka mutu a NIjeriya cikin mako guda sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da sauran tashe-tashen hankula wanda ke matsayin ...
Akalla mutane 101 suka mutu a NIjeriya cikin mako guda sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da sauran tashe-tashen hankula wanda ke matsayin alkaluma mafi yawa da kasar ta gani cikin makwanni 8 a jere.
Alkaluman da jaridar Premium Times
ta wallafa ya nuna yadda aka samu karuwar kasha 200 idan aka kwatanta da
alkaluman makon jiya da aka samu rasa rayukan mutane 32 sakamakon hare-haren.
Cikin mutanen 101 har da Basaraken gargajiya
da ‘yan bindiga suka kashe a Kaduna kana manoma 45 a Nasarawa sai kuma wasu
mutum 38 da ‘yan bindiga suka kashe a Kaduna.
Alkaluman na Premium Times ya nuna
cewa mabaMbantan hare-hare 8 ne ya kai ga kashe mutanen 101 a shiyyoyin arewa 3
dukkaninsu.
A wasu mabambantan hare-hare a
Zamfara, ‘yan bindigar sun kashe mutane 2 tare da kora tarin dabbobi a Tungar
Bai yayinda suka kashe wasu mutum 7 a Katsina baya gas ace wasu da dama.
Can a karamar hukumar Giwa ‘yan
bindiga sun harbe wani Magaji Ibrahim har lahira sa’o’I kalilan bayan sun kashe
mutane 38.
No comments