Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

CIRE TALLAFIN FETUR: Ƙungiyar Ƙwadago Ta Shirya Zanga-Zangar Ƙasa  

  Majalisar Zartwarwa ta Ƙasa ta ƙungiyar ƙwadago a Nijeriya ta yanke shawarar gudanar da zanga-zangar baki ɗaya a ranar 1 ga watan Fabarair...

 


Majalisar Zartwarwa ta Ƙasa ta ƙungiyar ƙwadago a Nijeriya ta yanke shawarar gudanar da zanga-zangar baki ɗaya a ranar 1 ga watan Fabarairu mai zuwa game da yunƙurin gwamnati na cire tallafin man fetur.

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar bayan taro da shugaban Nigeria Labour Congress (NLC), Ayuba Wabba, ya fitar ranar Juma'a.

NLC ta ce kafin gudanar da zanga-zangar ta ƙasa, za ta shirya maci a jihohin ƙasar 36 ranar 27 ga watan Janairu duka don matsa wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan kar ta cire tallafin.

'Yan ƙwadagon sun ce cire tallafin man zai jefa ma'aikata da sauran 'yan ƙasa cikin ƙunci sannan ya haifar da tashin farashin kayayyaki.

"Saboda haka Majalisar Zartwarwa ta yi watsi da yunƙurin gwamnati na ƙara kuɗin fetur saboda ya saɓa wa halin ƙuncin rayuwa da ma'aikata da sauran 'yan ƙasa ke ciki a yanzu," in ji sanarwar.

No comments