Cristiano Ronaldo ya zama dan wasa na farko a tarihi da ya zura kwallaye 800 a matakin manyan wasanni bayan da ya jefa kwallay...
Cristiano
Ronaldo ya zama dan wasa na farko a tarihi da ya zura kwallaye 800 a matakin
manyan wasanni bayan da ya jefa kwallaye biyu a wasan da Manchester United ta
doke Arsenal da ci 3-2 a gasar firimiyar Ingila a jiya Alhamis, tarihin da babu
wanda ya kafa gabanin shi.
Ronaldo
mai shekaru 36, ya zarta kowanne dan wasa wajen yawan kwallaye a wasannin kasa
da kasa da kuma gasar cin kofin zakarun Turai.
Kazalika
har yanzu babu wani dan wasa da ya ci wa Real Madrid kwallaye masu yawa kamar
Ronaldo, inda ya jefa mata kwallaye 450.
A
jumulce, dan wasan ya ci wa Manchester United kwallaye 130, idan aka hada da
zamansa na farko a kungiyar, sannan ya ci wa Juventus kwallaye 101, ya kuma
zura biyar a Sporting Lisbon, baya ga kwallaye 115 da ya ci wa kasarsa ta
Portugal.
Dan
wasan dai ya cire wa Manchester United kitse a wuta a wasanta na jiya da
Arsenal, yayin da ake ganin rawar da ya taka tamkar aike sako ne ga sabon kocin
kungiyar Ralf Rangnick wanda ake ganin ba lallai ba ne ya samu jituwa da
Ronaldo.
Sai
dai sabon kocin na rikon kwarya wanda ya halarci Old Trafford domin kallon
wasan na jiya , ya nuna gamsuwarsa da kwazon da Ronaldo din ya nuna a jiya.
No comments