Juan Cuadrado ya ci wata kyakkyawar kwallo a yayin da Juventus ta lallasa Genoa, lamarin da ya kai ta matsayi na 5 a teburin Ser...
Juan Cuadrado ya ci wata kyakkyawar kwallo a yayin da Juventus ta lallasa Genoa, lamarin da ya kai ta matsayi na 5 a teburin Serie A.
Tsohon dan wasan gefe na Chelsea din ya ci kwallo ne kai tsaye daga bugun kusurwa a cikin minti na 8 da fara wasa.
Paulo Dybala ya ci wa Juventus kwallo ta biyu,. Bayan da ya saka kwallon a ragar mai tsaron gida Salvatore Sirigu, a wasan da Juventus ta mamaye.
Genoa dai ba ta taka rawar gani a wasan ba, inda ma ta kasa kai ko da hari daya mai kyau, kuma yanzu tana matsayi na 18 a teburin gasar Serie A.
Genoa ta gaza cin ko da kwallo daya a cikin wasanni 4 da ta buga tun da Andriy Shevchenko ya zama kocinta.
Da wannan nasarar ta Juventus, tawagar ta Massimiliano Allegri ta samu nasara a wasani 5 cikin 6 da ta yi kenan.
No comments