Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta yi gargadin cewa sabon nau’in cutar Korona na Omicron na iya kassara tsarin kiwon lafiya a sassan duniya,...
Hukumar
lafiya ta Duniya WHO, ta yi gargadin cewa sabon nau’in cutar Korona na Omicron
na iya kassara tsarin kiwon lafiya a sassan duniya, duk da cewa binciken farko
ya nuna yana nau’in Koronar na Omicron,
ba shi da tsanani kamar sauran nau’ikan annobar.
Rahoton
RFI ya ce; hukumar WHO ta yi wannan gargadi ne a yayin da China da kasashen
Turai da kuma Amurka suka dawo da tsauraran matakan dakile yaduwar Korona,
sakamakon hauhawar masu kamuwa da cutar.
A
kasar Amurka gwamnati ta rage lokacin killace wadanda suka kamu da cutar Korona
da basu tagayyara ba domin warware matsalar cinkoso a asibitoci.
A
Faransa kuwa inda aka ga hauhawar masu Korona da adadin mutane fiye da dubu 100
a baya baya nan, gwamnati ta umarci hukumomi da kamfanoni da su sa ma'aikata su
yi aiki daga gida tsawon akalla kwanaki uku a mako.
Ita
kuwa Jamus ta maido ne da dokar takaita walwala ta hanyar rufe wuraren
shakatawa na dare, da kuma tilasta gudanar da wasanni ba tare da ‘yan kallo ba.
Duk
da fuskantar karancin barkewar cutar idan aka kwatanta da wuraren da annobar ke
sake yin kamari a sassan duniya, kasar Sin ba ta sassauta matakan dakile
yaduwar Koronar ba, inda a baya bayan nan ta maida dokar kulle a sassa da dama
na birnin Yan'an, mataki mafi tsauri da ta dauka bayan garkame birnin Wuhan da
ta yi a farkon barkewar annobar.
Alkaluma
sun nuna sabon nau’in Korona na Omicon shi ne yayi tasiri wajen karuwar masu
kamuwa cutar a akasarin kasashen musamman na Turai, inda a baya bayan nan Netherlands
da Switzerland suka tabbatar da cewar Omicron din ne ya zarce sauran nau’ikan
Koronar yawaita a cikinsu, yayin da kuma Girka ta ba da rahoton gano mutane
dubu 21,657, da suka harbu da annobar cikin rana guda.
No comments