Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Cututtuka 11 Da Shaikh Zakzaky Da Matarsa Ke Dauke Da Su Sakamakon Harbinsu -Likita

  Daga Ammar M. Rajab   Dr Abubakar Yahaya, daya daga cikin likitocin jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai d...


 
Daga Ammar M. Rajab 

Dr Abubakar Yahaya, daya daga cikin likitocin jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim ya bayyana kalaman babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) kuma ministan shari'a Abubakar Malami akan yanayin lafiyarsu a matsayin rashin gaskiya da karya tsagwaronta.


Dakta Yahaya ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, a cikin wata sanarwa da aka aikowa da MADOGARA a Abuja mai taken: “Rike Fasfo din Shaikh Zakzaky, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, na da hannu a ciki.”


Ya ce da rahoton kafar yada labarai ta ruwaito Malami na cewa a ranar 22 ga watan Nuwamba, 2021, cewa yanayin rashin lafiyar ma’auratan da aka ce yana da hatsari ga rayuwarsu, ba gaskiya bane. A cewarsa, wadannan maganganun karairayi ne da Malami ya fada wanda ya yi hakan ne saboda Abubakar Malami yana son lullube laifuffukansu da dama.


“ina rubuto wannan ne a madadin Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah Ibraheem domin na daidaita lamarin. Sabanin abin da Malami ya yi ikirari, haƙiƙa akwai sabbin shaidun da ke tabbatar da cewa dukansu su biyun suna fama da matsalolin rashin lafiya da dama da ke da matuƙar hadari, kamar yadda sakamakon gwaje-gwajen da suka yi na likitanci wanda aka saba gudanar na yau da kullum ya nuna tun 2018 (bayan Shehin Malamin ya samu bugun jini na farko, wanda a karshe hukumar DSS ta ba da damar samun Likitocinsu a karon farko), sannan abin ya ci gaba har zuwa shekarar 2020 da 2021.

"Muna da takardun da suke tabbatar da abin da muka fada. “Gwajin da aka gudanar a shekarar 2019 ba wai kawai zargi bane ko karin gishiri, a’a a zahiri ma cibiyoyin kiwon lafiya ne na gwamnati da aka amince da su suka gudanar da gwajin, wanda ke nuni da cewa mutanen biyu na fama da cututtukan da a yanayinsu a yanzu yana da bukatar kulawar gaggauwa kuma barazana ne ga rayuwarsu, kamar yadda kwararrun likitocin suka tabbatar daga ciki da wajen Nijeriya - ciki har da wadanda hukumar DSS ta gabatar.

 “a bisa gaskiya, rahotan gwajin da likitoci suka yi musu na baya-bayan nan (24 ga Satumba, 2021) an jera cututtuka masu yawa har guda goma sha daya waɗanda har yanzu Shaikh Zakzaky ke fama da su, wato: “Ciwon zuciya, girma da tabewar tsokar zuciya da ke harba jini zuwa sassan jiki (wanda hakan ke rage aikin ta), fashewar jijiyar kwakwalwa a sashen ‘thalamus’ hagu da dama (wanda ke haifar da shanyewar rabin jiki), qanqancewar kofofin kashin baya (inda lakka ta shiga) na sashen wuya da ciki, wanda ke haifar da matsanancin ciwo; rashin idon bangaren hagu, yanar ido mai hayayyafa ta bangaren idon dama; girma da hayayyafar ‘prostate’ (wanda zai iya haifar da ciwon sanqara/daji); gubar dalma da ‘cadmium’ mai tsanani, rauni ga tsokokin jiki da sauran sassa masu taushi, karafa a sassan jiki daga harbin da aka yi masa (gutsitstsiran alburushi sun kai 55 har yanzu ba a cire ba daga jikin Shaikh) a qoqon kai, kurmin ido, tsintsiyar hannun hagu da kuma gefen cinya; sai kuma matsalar rashin daidaiton kitse”.

“Matarsa Malama Zeenah a rahoton gwajin likitoci na baya-bayan nan da aka yi mata (24 ga watan Satumban 2021, gwajin ya nuna tana fama da haduwar cututtuka guda goma sha daya da suma suke da matukar hatsari; cututtukan sune: ciwon hawan jini mai tsanani wanda magani ya kasa sakko da shi, rugurgujewar kashin gwiwa mai tsanani- na duka kafa biyu (wanda ya haddasa ta koma amfani da kujerar turawa tsawon shekaru 4 yanzu) wanda kuma yana buqatar a yi tiyata a sake qoqon gwiwar baki daya, ciwukan tsokoki da sauran sassan jiki masu taushi daga harbin alburushi, yawaitar ciwon ciki mai tsanani wanda ke da alaqa da harbin da aka yi mata (baqin alburusai a cikin ta); ‘gastritis (inflammation na ciki); kumburin hanta wanda ba a san dalilin da ya kawo shi ba; sanqarar mahaifa marar tsanani; matsalar kashin bayan ido na bangaren hagu (ya kamu da kwayar cuta); matsalar rashin daidaiton kitse; bayyanar qullutu a mama (nonon) ta na bangaren dama da kuma kumburin ‘lymph node’ da ke kusa da maman (ana tsoron kamuwa da sankarar mama); da kuma taruwar ruwa a kodar ta ta bangaren dama”.

Ya ce kwararre a fannin kiwon lafiya da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kawo shima ya tabbatar da wasu cututukan da ma’auratan ke fama da su da ake danganta su da karafa masu nauyi.

"a don haka abin damuwa ne da rashin mutuntawa a ce hukumomin da abin ya shafa har yanzu suna tilasta wa mutanen biyu su ci gaba da zama a Nijeriya, inda babu wani cikakken kulawa na magani a asibitin (Nijeriya) game da irin wadannan guba (dake jikinsu) da dukkanin cututtukan da aka lissafa," in ji shi. Yahaya ya bayyana cewa hukumar DSS da kotu da sauran hukumomin da abin ya shafa suna sane da tabarbarewar rashin lafiyarsu.

“A gaskiya saboda sakamakon binciken da likitoci suka yi a shekarar 2019 ne ya sa a karshe babbar kotun Kaduna ta bayar da umarnin a kai dukkansu asibiti domin yi musu aikin tiyata da magani yadda ya kamata.

 “Tawagar kwararrun likitocin da suka hada da wadanda DSS da gwamnatin jihar Kaduna suka aiko a lokacin, sun tabbatar da cewa Shaikh da matarsa suna da munanan cututtuka har guda 8 da kuma cututtuka 6 masu hatsarin gaske a lokaci guda.

 “Har ila yau, a bisa gaskiya kuma kokarin da aka yi na yi musu magani a Indiya an (gwamnati ta) hargitsa shirin baki daya kuma jami’an tsaron da suka yi tafiya tare da su ne suka dawo da su Nijeriya.

 “Tun da suka dawo daga Indiya, babu wani abu daga cikin abubuwan da ake da bukata da aka yi wa Shehin Malamin ko matarsa, kuma har yau ana nan a hakan.

"Duk da kokarin da likitocinsu suke yi, yanayin lafiyarsu dangane da wadannan cututtukan na kara tabarbarewa, a sakamakon haka har yanzu suna bukatar gaggawar samun wadannan magunguna a wajen Nijeriya, kamar yadda aka saba kuma har yanzu masana ne ke ba da wannan shawarar," in ji shi.

A cewarsa, sabanin ikirari na karya da Abubakar Malami ya yi na cewa babu daya daga cikin likitocin su da ya yi wani gwaji, musamman likitocin biyu da aka ambata, a zahiri an gudanar da gwaje-gwajen ne ta hanyar dakunan gwaje-gwajen asibiti da gwamnati ta amince da su, wanda ya nuna sabon binciken da aka samu a Asibitin Malam Aminu Kano da Asibitin koyarwa na Barau Dikko (AKTH/ Barau Dikko Teaching Hospital a shekerar 2020 da kuma Synlab Abuja a shekarar 2021), sakamakon bai sauya ba ko daya daga cikin abin da aka bukata na kulawar asibiti/tiyata waɗanda aka bayar da shawara ga dukkansu tun a cikin shekarar 2019.

Ya bayyana cewa, duk kokarin da ake yi kan Zakzaky da matarsa a baya-bayan nan na magani abin ya ci tura ya zuwa yanzu sakamakon rashin fasfo na kasashen waje.

“samar da takardun tafiye-tafiye da sauran dukkanin abin da ake da bukata a kasashe da ake sa ran za a yi musu tiyata da sauran kulawar lafiya, bisa shawarwarin da dukkanin kwararru likitoci da suka yi nazari akan matsalarsu ya zuwa yanzu.

“A gaskiya ma, ikirarin da Malami ya yi na cewa babu bukatar gaggawa ga ma’auratan na zuwa kasar waje domin duba lafiyarsu ya kara tabbatar da cewa yana da hannu wajen hana su fasfo da sake ba su wasu sabbi.

“Ya kamata wakilin tsokanar ya lura da cewa ko da ko babu rashin lafiyar, Shaikh Zakzaky da matarsa suna da ‘yancin mallakar fasfo na Nijeriya da kuma tafiya duk inda suke so.

“Yana daga cikin hakkokinsu, sai dai idan Abubakar Malami doka ne shi a kashin kansa," in ji Yahaya.

No comments