Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Da Amincewar Malam Aminu Kano Muka Tsige Balarabe Musa, Cewar Tsohon Kakakin Majalisar Jihar Kaduna

-Alhaji Mamman Abubakar Danmusa A hirar musamman da jaridun KATSINA CITY NEWS suka yi da Alhaji Mamman Abubakar Danmusa, tsohon...

-Alhaji Mamman Abubakar Danmusa

A hirar musamman da jaridun KATSINA CITY NEWS suka yi da Alhaji Mamman Abubakar Danmusa, tsohon Kakakin Majalisar tsohuwar Jihar Kaduna, kuma mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa a jamhuriya ta uku, inda ya bayyana mana tarihin rayuwarsa da kuma tsokaci a kan wasu lamurran tarihi da suka faru a baya.

Danmusa ya bayyana cewa a lokacin da suka tsige Balarabe Musa a daga Gwamnan Kaduna, sai da suka samu cikakken goyon bayan uwar jam’iyyarsa ta PRP, wadda shugabanta, Malam Aminu Kano ya karfafa masu gwiwa.

Danmusa ya ce a lokacin, duk da PRP ce ta tsayar da Balarabe Musa, amma sai ya zama yana amsar shawarwari ne daga ‘yan jam’iyyar UPN ta Awolowo.

Ya ce; “PRP ta ba shi tsarin da zai zabi Kwamishinoni, shi kuma ya biye wa shawarawarin ‘yan UPN, ya ki bin abin da suke so. Wannan ya sa duk lokacin da ya kawo sunayen Kwamishinonin da za a nada, duk Majalisar sai ta ki amincewa.”

Danmusa ya ce Balarabe Musa bai iya siyasa ba, kuma ya raina ‘yan Majalisa, shi da Yusuf Bala Usman, Sakataren gwamnatin lokacin, sun dauki ‘yan Majalisar ba su da ilmin Boko ne. Wannan ya sa Majalisar ta hade masa kai.”

Danmusa ya ce; “Lokacin da muke kokarin tsige Balarabe Musa, sai muka lura matsalarmu daya ce. Sai na rubuta takarda na kori Yusuf Bala Usman daga Sakataren gwamnatin.

“Manufata in dauke masa hankali, kar ya kawo mana cikas ga aikinmu. Hakan kuma aka yi. Bala Usman ya rude, ya cika kasa da surutu da kokarin tabbatar wa cewa ban isa in kore shi ba a doka.

“Kafin ya ankara har mun gama aikinmu. Dama wayau muka yi masa, don mu dauke masa hankali, kar ya kawo mana cikas. Don shi kadai muke shakka,” in ji shi.

Danmusa ya yi watsi da wata jita-jita da ake yadawa ta cewa ya taba marin Balarabe Musa. Ya ce; “Wannan ba gaskiya ba ne. Ni ban mari Balarabe Musa ba. Ya so ya raina ni ne, ya tozarta ni a garinmu, sai na nuna masa ya yi kadan.”

No comments