Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Dan Majalisa Mai Wakiltar Hadejia Ya Samu Nasara Kan Kudurin Cin Zarafi Yara Kanana

Dan majalisa mai wakiltar Hadejia A majalissar Jihar Jigawa Barista Abubakar Sadiq Jallo,  ya samu nasarar ian kudirin da ya sha...


Dan majalisa mai wakiltar Hadejia A majalissar Jihar Jigawa Barista Abubakar Sadiq Jallo, ya samu nasarar ian kudirin da ya shafe tsawon shekaru takwas a gaban majalisar jihar, inda ya zama doka kuma Gwamna Badaru ya rattaba hannu akai.

Cikin Shiri na Musamman da ya zanta da SAWABAFM, Jallo ya kawo irin kai wa ruwa rana da kudirin ya dade yanayi a gaban majalisar, har kuma wannan lokacin aka kai ga nasara.

Barr. Abubakar Sadiq Jallo ya kawo batun dokar inda ya bayyana cewa, dokar a farko an kasa fahimtarta ne wasu suna mata kallo a matsayin ta cin karo da addinin Islama.

Jallo ya kawo cewa sun kirkiri kwamiti na musamman wanda ya kunshi manyan Malaman Musulunci ciki kuwa harda Babban malamin addinin musulunci  Dr. Abubakar Sani Birnin Kudu da Dr. Turaki Usman Hadejia dama kwararru daga Hukumar UNICEF.

Jallo ya kara da cewa cin zarafin yara ya hada da aikata fyaɗe ga yara ƴan kasa da shekara goma, auren wuri, sawa yara sunan nanza, yin zanen bata fuska da sauran su. 

Barista ya kawo matsala yadda al'umma take fama da rashin tarbiyya wanda hakan ya samo asali ne daga haihuwar ƴaƴan marasa iyaye.

Jallo ya kara da cewa ya zuwa yanzu duk wanda ake zargi da aikata haihuwar yaro bada aure ba, kuma mutum ya ki karbar yaron za a gudanar da gwajin kwayar hallita wato DNA.

Dokar ta kara da cewa duk wanda aka kama ya yi wa yara kanana fyade, za a masa hukuncin kisa inda a da ake yanke hukunci daurin rai da rai.

Haka kuma dokar ta hana yi wa yara kanana zanen a fuska. 

Ya zuwa yanzu dai za a iya cewa Barista Jallo ya cimma gagaruma nasara kasancewar kudurin ya dade yana reto a gaban majalisar.

No comments