Tsohon Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya yi kira ga 'yan majalisar dattawa da su yi gaggaw...
Tsohon Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya yi kira ga 'yan majalisar dattawa da su yi gaggawar yin abin da ya dace tunda Shugaba Buhari ya bayyana matsayarsa ta ƙin rattaba hannu kan ƙudurin dokar Zaɓe.
Saraki ya yi wannan kira ne a wata takardar sanarwar manema labarai da ya fitar jiya Laraba a Abuja.
Tsohon gwamnan na Kwara ya ce, tabbas yana magana ne a madadin miliyoyin 'yan Nijeriya, ta hanyar ɗaukar matakin gaggawa.
Ya ce: "Ba zai yiwu mu zuba ido kawai wata 'yar matsala dake cikin ƙudurin zaɓe ta hana a zartas da wannan ƙuduri ba. Majalisa tana zaɓin yin abin da ya dace, ko dai su yi kunnen uwar shegu da ƙin amincewar shugaban ƙasa, ko kuma su cire batun zaɓen 'yar tinke wurin fidda gwani su sake aikawa shugaban ƙasa da shi.
"Kowanne a ciki suka ɗauka, 'yan majalisa za su iya yin abin da ya dace cikin kankanin lokaci. Za mu iya samun sabon dokar zaɓe a Janairun 2022.
"Duk wanda ke bibiyar ra'ayoyin 'yan Nijeriya zai fahimci cewa suna matuƙar shauƙin samun sabon dokar zaɓen da zai bayar da damar yin zaɓe mai tsafta, kuma cikin kwanciyar hankali. Suna buƙatar tsarin da zai tabbatar da an kirga kuri'unsu don zaɓan shugabanni." Inji shi
No comments