Duk da natsalar tsaro da ake fama da shi musamman a Arewacin Nijeriya a kuma daidai lokacin da wasu ke fafutikar jawo hankalin g...
Duk da natsalar tsaro da ake fama da shi musamman a Arewacin Nijeriya a kuma daidai lokacin da wasu ke fafutikar jawo hankalin gwamnati ta hanyar zanga-zangar lumana kan halin da yankin yake ciki, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yo bukin murnar ranar haihuwarsa.
Shugaban a yayin bukin yyace zai mayar da hankali wajen ci gaban Nijeriya da al’ummarta kafin Æ™arshen wa’adinsa.
Shugaban ya bayyana hakan ne tare da hotunan bikin zagayowar haihuwarsa a Turkiyya a shafin Facebook.
"Ina fatan zuwa 2023 idan na kammala wa’adina na koma gida na kula da gona ta. Amma kafin nan zuwa lokacin zan yi iya Æ™oÆ™arina wajen ciyar da Æ™asa da al’ummarta gaba da gudanar da ayyuka kamar yadda kundin tsarin mulkin Æ™asa ya tanada,” kamar yadda shugaban ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya ce ashe bai guje wa bikin haihuwarsa ba a Abuja kuma haka ma a Turkiyya sai da aka haÉ—a masa bikin.
A ranar Juma’a ne shugaba Buhari ya cika shekara 79 da haihuwa. Kuma tun a ranar Alhamis ya tafi Turkiyya.
No comments