Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Faransa Ta Soke Wasan Wuta Na Sabuwar Shekara Saboda Omicron

Gwamnatin Faransa ta soke bikin wasan wuta da aka saba yi na sabuwar shekara a kasar, sakamakon hauhawar masu kamu da cutar Koro...


Gwamnatin Faransa ta soke bikin wasan wuta da aka saba yi na sabuwar shekara a kasar, sakamakon hauhawar masu kamu da cutar Korona a kasar, abinda kwararru suka danganta da sabon nau’in cutar na Omicron, wanda suka yi ittifakin shi ne musababbin sake barkewar annobar a sassan duniya da dama, musamman ma a nahiyar Turai.

Matakin Faransa na soke bukukuwan sabuwar shekara ya biyo bayan shawarar da wani kwamitin kimiyya da ke nazari kan matakan dakile yaduwar annobar Korona.

A baya bayan nan ne dai shugabar hukumar gudanarwar kungiyar EU Ursula von der Leyen ta yi gargadin cewa sabon nau’in Korona na Omicron ka iya zama mafi rinjayen yaduwa akan saauran nau’ikan cutar a nahiyar Turai, nan da tsakiyar watan Janairun da ke tafe.

Tuni dai kasashe da yawa suka yanke shawarar sake dawo da matakin takaita tafiye-tafiye da wasu takwarorinsu tun bayan fara gano sabon nau’in Korona na Omicron a Afirka ta Kudu.

A ranar Juma'a, Jamus ta aayyana Faransa da Denmark a matsayin yankuna masu hatsarin gaske kuma ta ce matafiya da ba su da rigakafin dole ne su kebe da zarar sun shiga kasar.

-RFI

No comments