Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

GA WATA DAMA: Manoman Nijeriya Za Su Samu Rancen Dala Miliyan 210

Bankin raya kasashen Afirka, AfDB za ta ba wa kananan manoman Nijeriya tallafin rancen kudade dala miliyan 210 da zimmar bunkasa...



Bankin raya kasashen Afirka, AfDB za ta ba wa kananan manoman Nijeriya tallafin rancen kudade dala miliyan 210 da zimmar bunkasa ayyukan noma da harkokin kiwo a fadin kasar kamar yadda DW ta labarto. 

Wannan shi ne tallafi na farko karkashin wani shiri na musamman da bankin raya kasashen Afirka ta bullo da shi don rage wa manoma tsadar kaya. 

Shirin zai fara ne da jihohi bakwai na Nijeriya, sannan daga baya za a fadada shirin zuwa wasu kasashen Afirka guda bakwai.

A yayin taron zuba jari a kasar Saudiyya a watan Oktoba na shekarar 2021, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce Afirka ce ta fi ko ina yawan kasar yin noma. 

Sauran abokan hulda kamar Bankin Raya kasashen Musulunci da kuma asusun bunkasa noma na kasa da kasa, za su hada hannu wajen tallafawa aikin.

Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce Nijeriya na da yawan gonaki sai dai kasar  na dogaro ne da shigo da kaya daga waje don ciyar da al'umarta fiye da mutane.

No comments