Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gidaje Kusan Miliyan Daya Aka Rasa A 'Yakin Boko Haram'

Gwamnatin jihar Borno ta ce gidajen ɗaiɗaikun mutane fiye da dubu 956 ne aka rasa a tsawon shekarun da aka yi na rikicin Boko Ha...


Gwamnatin jihar Borno ta ce gidajen ɗaiɗaikun mutane fiye da dubu 956 ne aka rasa a tsawon shekarun da aka yi na rikicin Boko Haram.

Adadin ya yi daidai da kimanin kashi ɗaya cikin uku na ɗaukacin gidajen da ke faɗin jihar. 

Tsawon shekara 12 kenan a na dauki-ba-dadi tsakanin dakarun Najeriya da kungiyar Boko Haram a wasu jihohin Arewa maso Gabashin Najeriyar, da suka hada da Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Kuma a tsawon wannan lokaci an rasa rayuka da dukiya mai dimbin yawa, sannan miliyoyi sun rasa matsugunansu.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnatin ta jihar Borno Isa Gusau ya fitar, ya kuma ce an yi asarar gine-gine sama da 660 mallakar hukumomi daban-daban, sanadin wannan rikici na 'yan ta-da-ƙayar-baya.

BBC ta fahimci cewa gine-ginen da aka rasa mafiya yawa ofisoshin hukumomi ne da suka hada da gidajen yari, da ofisoshin 'yan sanda da kuma makarantu.

Isa Gusau ya kara da cewa duka bayanan da suka samu wani ɓangare ne na rahoton kimanta ayyukan wanzar da zaman lafiya da farfaɗowa na Bankin Duniya kan yankin Arewa maso Gabas.

"Ba inda aka fi rusa gidaje kamar Bama daga cikin kananan hukumomi 20 da wannan abu ya faru.

"A halin yanzu daga hawansa zuwa yanzu Zulum ya gina gidaje 10,000, kuma ana nan an sake tsugunar da 'yan gudun hijira a garuruwa kusan 18," in ji Isa Gusau.

Sai dai batun sake tsugunar da 'yan gudun hijirar ya haifar da ce-ce-ku-ce musamman a tsakanin kungiyoyin jin-kai, inda wasunsu ke ganin har yanzu babu tsaron da za a kafa hujja da shi na sake mayar da 'yan gudun hijirar garuruwansu.

Jihar Borno ta fi kowace jihar jin jiki a yaki da kungiyar Boko Haram tsawon shekaru, sai dai gwamnati mai ci ta Farfesa Babagana Umara Zulum na da burin ganin ta sake mayar da 'yan gudun hijira garuruwansu na asali, tare da kuma tallafa musu da kayan lalurar yau da kullum.

A wata mai kama da haka gwamnan ya roki masu kwatanta ayyukansa da na sauran gwamnoni su daina.

A wata sanarwar ta daban da mai magana da yawun nasa, Isa Gasau ya fitar ranar Litinin gwamnan ya yaba wa mutanen da ke tallata ayyukansa a shafukan sada zumunta, sai dai ya ce bai kamata a rika kwatanta "ayyukana da na sauran gwamnoni ba, tun da dukkan jihohin suna da bambanci.''

"Duk da yake Ina matukar godiya bisa dukkan goyon baya da tallata ayyukana, a kwanakin nan na samu sakonni, inda ake kwatanta ayyukan da muke yi a Borno da na wasu jihohi, a wasu lokutan ma ana zagi.

Gaskiya ba na jin dadi a duk lokacin da aka kwatanta ni da wani gwamna ta hanyar muzanta shi, musamman idan wadanda suke yin hakan, suna cikin masu amfani da shafukan sada zumuntar da ke da alaka da mu", in ji Gwamna Zulum.

No comments