Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gina Jami’ar MAAUN Da Farfesa Gwarzo Ya Yi Cigaba ne Ga Al’umma– Sheikh Al-ƙarmawi

Daga Ali Kakaki Shehin Malamin addinin Musuluncin nan na garin Kano, Sheikh Abdulwahid Muhammad Nazifi Al-ƙarmawi ya yaba da kok...


Daga Ali Kakaki

Shehin Malamin addinin Musuluncin nan na garin Kano, Sheikh Abdulwahid Muhammad Nazifi Al-ƙarmawi ya yaba da kokarin Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa kafa Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake garin Kano, inda ya ce tabbas ginin Jami’ar ya ginu, kuma komai ya wadatu, kuma abin a yaba wa Farfesa A.A Gwarzo ne bisa namijin kokarin da ya yi wajen kafa Jami’ar domin amfanar mutanen jihar Kano da Nijeriya da duniya ma baki daya.

Sheikh Abdulwahid Muhammad Nazifi Al-ƙarmawi ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kawo Jami’ar, inda aka zagaya da shi fanno da bangare daban-daban a cikin Jami’ar dake Kano.

Sheikh Al-ƙarmawi ya bayyana cewa makasudin kawo ziyarar shi ne; “domin kara karfafar harkar ilimi da kuma farin ciki da samun ci gaba wanda Allah ya bamu a kasarmu. Kuma mu ne masu amfanar abin da kuma yaranmu da sauran ‘yan’uwa”, ya lurantar.  

Har wala yau a wani bangare na bayaninsa, Al-ƙarmawi  ya ce; “gaskiya wannan Jami’a, jami’a ce wacce na zagaya na ga iya inda muka iya kewayawa, mu ka ga kowanne irin bangare, Alhamdulillah. Abu ya yi. Gini ya ginu, kuma komai ya yi, mun yi addu’a kuma yadda Allah ya gina mana wannan Jami’a, Ubangiji Allah ya gina mana albarka ya zuba hasken Annabi Muhammadu a ciki. Ya cika da farin ciki. Wannan Jami’ar ba a Nijeriya ba, ballantana a Kano, ko a wata kasa mu ka je mu ka ganta, za mu ji dadi mu yi farin ciki saboda abu ne na amfanar al’umma, kuma ci gaba ne na bayin Allah”.

Shehin Malamin ya ci gaba da cewa; “shi Farfesa namu na Gwarzo, Allah ya saka masa da alheri. Kuma ya kara masa karfin guiwa, kuma ya kara karfafarsa a zahiri da badinin niyyarsa ta alkhairi. Domin wannan babu abin da zai janyo irin wannan aikin sai niyya ta alheri da kyawun zuciya. Muna rokon Allah ya saka masa ya kuma kara karfafarsa. Kuma shekarunsa ba yawa, muna rokon Allah ya kara masa shekaru masu yawa, ya tsufa ya yi shekaru masu yawa yana ci gaba da wannan aikin da al’umma za ta amfana. Muna rokon Allah ya wanzar da amfanin irin wadannan ayyuka na shi har ya zuwa ranar alkiyama, al’ummar Annabi (S) su dinga amfana da shi” ya yi addu’a.

Kazalika, Sheikh Abdulwahid Al-ƙarmawi, ya ja hankalin al’umma akan muhimmancin neman ilimi, inda ya ce rayuwa baki dayanta ba ta kyau sai da ilimi, inda ya ce akwai bukatar al’umma ta tsaya ta nemi ilimi domin ci gaba; “duk wani abin da ake gani na ci gaban nan, ko wannan aikin, ilimi ne. Saboda haka ina jan hankalin ‘yan’uwa a tsaya a kan ilimi, kuma a tsaya a taimakawa yara musamman iyaye maza da mata a tsaya a ga yara sun tsayawa ilimi domin amfanin ilimi ta duk inda bawa ya bullo dai rayuwarsa ta na shan bamban da marasa ilimi”, ya jaddada.

Ya karfafa iyayen akan muhimmancin neman ilimi ga ‘ya’yansu da cewa; “mun sani cewa Malamanmu sun tabbatar mana da abin da suka gani kuma da abin da suka samu a nassoshi cewa rayuwar mara ilimi, mutuwa ce. Kuma rayuwar mai ilimi, rayuwa ce, kuma mutuwarsa rayuwa ce. Duk wanda ya zama ya samu ilimi, to yana nan da rai, ba zai mutu ba. Domin ko da an ce ya yi mutuwar da ake yi, to ambatonsa da fadin alheransa ba zai kauce ba matukar rayuwa, idan ko ambaton bawa bai kauce ba, to fa bai mutu ba da ilimi”, ya tabbatar.

Ya kara da cewa; “sannan idan neman jindadi bawa ke yi, dole ya yi ilimi. Masu iya magana suka ce da an yi ilimi ba zancen talauci, ba zancen wai-wai. Damuwar zuciya, bakin ciki, mugun hali, shiga cikin wayyo, in dai an yi ilimi babu su. Saboda haka musamman iyaye a karfafi yara da karatu, kuma a tsaya tsayin daka a ga yara har matan ma duka a tsaya a tabbatar da an ga sun yi karatu”.

Da yake karfafa muhimmancin ilimi ‘ya’ya mata kuwa, Sheikh Abdulwahid Al-ƙarmawi cewa ya yi; “gudun karatu da ake yi na mata da cewa mata ba a bari su yi karatu, tsoron tarbiyyah, ba sa barin gida da sauran su, to tarbiyyah ta asali tun daga gida ne. Idan ka raini yaronka a tarbiyyah Islamiyyah Muhammadiyyah, to shi ke nan duk inda zai tafi ya je in dai ya rike tarbiyyar nan kuma an tabbatar masa da tarbiyyar nan, mace ce ko namiji, za a rayu lafiya. Amma rashin tarbiyyah shi yake bata rayuwar yaranmu maza ko mata. Ko ba a bar yarinya ta je makaranta ba, in dai ba a yi mata tarbiyyah Muhammadiyyah Islamiyyah ba, tana gidan ma ta zama lalatacciya, nawa aka yi?”, ya tambaya.

Ya karfafa da cewa; “mu dai mu kyautata niyya, kuma mu yi wa Allah kyakkyawan zato, duk inda yaranmu suke, maza ne, mata ne, inda duk za su shiga, mu bar wa Allah albarkar Annabi (S) Allah ya rike mana, kuma mu tarbiyyantar da su, shi ke nan. Saboda haka ina karfafar ‘yan’uwa mu tsaya ma karatu. Dukkanin wani geji da mutum ya kai idan ba don karatu ba, ba a kai wa”, ya jaddada.

A karshe ya yi addu’ar wannan jami’a sabuwa da aka gina a Kano, Allah ya amfanar da mutanen Kano da ita; “Kuma Allah ya amfanar da mutanen Nijeriya duka da ita. Allah ma ya amfanar da dukkanin mutane na duniya da wannan Jami’a ta mu mai albarka. Kuma Allah ya kara taimako. Allah Ubangiji wannan ziyara tamu, Allah ya karba. Allah yasa ta zama sanadi na fatahi don albarkacin Manzon Allah. Farfesa kuma Allah ya saka masa, mataimakansa, tun daga kai kanka kai Kakaki, da duk mataimaka a wannan Harka, inda duk kuke a duniya, Allah ya dafa muku albarkacin Manzon Allah” ya karkare.

No comments