Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga gwamnatin Birtaniya da ta janye matakin hana shiga ƙasar daga Nijeriya saboda nau'in korona ...
Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga gwamnatin Birtaniya da ta janye matakin hana shiga ƙasar daga Nijeriya saboda nau'in korona na Omicron.
Ministan Yaɗa Labarai da Al'adu Lai Mohammed ne ya yi kiran yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, yana mai cewa "babu hikima a matakin".
Ya ce duk da cewa kwamatin yaƙi da korona na shugaban ƙasa zai ɗauki matakin da ya dace, "ni a matsayina na mai magana da yawun gwamnati ina kallon matakin a matsayin zalinci da horo".
Ya ƙara da cewa matakin na Birtaniya ba a ɗauke shi ta fuskar kimiyya ba, sannan ya bayyana mamakinsa kan "ta yadda za a ɗauki matakin kan ƙasa (Nijeriya) mai al'umma fiye da miliyan 200 kawai saboda tsirarun mutanen da suka kamu da cutar".
Ofishin jakadancin Birtaniya a Najewriya ya dakatar da bayar da biza ga 'yan Najeriyar sakamakon haramcin tafiyar da aka saka.
Shi ma kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na British Airways ya soke dukkanin tikitin shiga Birtaniya daga Najeriya, inda ya nemi fasinjojin su sauya lokaci ko kuma wurin tafiya.
-(BBC)
No comments