Daga Wakilinmu Garin Shinkafi dake karamar Hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara na fara da hare-haren 'yan bindiga fiye da kowa...
Daga Wakilinmu
Garin Shinkafi dake karamar Hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara na fara da hare-haren 'yan bindiga fiye da kowanne lokaci a 'yan kwanakin nan kamar yadda majiyarmu ta labartawa MADOGARA.
Majiyarmu da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana mana cewa a kwanakin nan; "An rutsa da garin Shinkafi rutsa mai tsananin gaske da garin bai taba fuskantar matsin ta'addancin 'yan bindiga kamar wadannan kwanakin masu tashin hankali da firgici ba".
Majiyar ta ci gaba da cewa; "Hanyar zuwa Shinkafi ta zama hanyar zuma kiyama. Babu ko shakka Gwamnati ta sallamawa 'yan ta'adda wannan gari mai albarka ta kewayensa. Wallahi kilomita daya ya yi nisa tsakanin 'yan ta'adda da garin Shinkafi musamman a shiyyata ta gabashin garin mai suna 'Yar Sakalawa", ya jadadda.
Ya kara sa cewa; "A wannan shiyyar har hangen baburansu ake yi, wani lokaci idan sun fara harbin ta'addancinsu har cikin shiyyar yake kawowa. Wannan masifar da mahukumta suka zurawa ido tare da rashin daukar matakin kawo karshenta to dole mu zarge su da amfana da ita" inji shi.
Ya karkare da cewa; "Muna rokon Allah duk mai amfana da kisan al'umma ko son cimma wata manufar siyasarsa, Allah gaggauta kawo mana karshensa cikin kaskanci da kunyata".
No comments