Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

IBB Na 'Goyon Bayan' Osibanjo A Zaben 2023

  Tsohon shugaban mulkin soji a Najeriya Janaral Ibrahim Babangida ya bayyana mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osibanjo da cewa mutumi...

 


Tsohon shugaban mulkin soji a Najeriya Janaral Ibrahim Babangida ya bayyana mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osibanjo da cewa mutumin kirki ne wanda yake da kyakkyawan fata ga kasar.

Tsohon shugaban ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da gidauniyar Osibanjo Grassroot ta kai masa a ranar Alhamis a birnin Minna na jihar Neja.

Gidan talbijin na Channels ya ambato Babangida na cewa “Na yi wa mataimakin shugaban kasar farin sani. Mutumin da yake da kyakkyawan fata ga Najeriya: mutumin da yake da kyakkyawar alaka da ‘yan kasa da ba su kwarin gwiwa.

Mutum irin wannan ya cancanci a yi aiki da shi. Muna bukatar mutumin kwarai ya jagoranci Najeriya. Mutumin da yak e kaunar kasar nan. Najeriya kasa ce ta kwarai, haka mutanenta. Yana da matukar muhimmanci ka fahimci al’ummarka, ta yadda za ka kyautata musu.’’

Janaral IBB ya mika sakon fatan alheri ga mataimakin shugaban kasar, ta hannun gidauniyar da ke fafutikar ganin Osibanjo ya tsaya takarar shugabancin kasar.

"Ina son ku shaida masa cewa ya ci gaba da abin alheri da yake yi. Na san ba abu ne mai sauki ba, amma yana da sigogin hakan. Ina masa fatan alheri,” in ji Babangida.

No comments