Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ina Daga Cikin Masu Zuga Mbappe Ya Bar PSG -Ibrahimovic

Zlatan Ibrahimovic ya tabbatar da cewa yana daya daga cikin mutane da suka zuga dan wasan PSG na Faransa Kylian Mbappe da ya bar...


Zlatan Ibrahimovic ya tabbatar da cewa yana daya daga cikin mutane da suka zuga dan wasan PSG na Faransa Kylian Mbappe da ya bar kungiyar dake taka leda a gasar Ligue 1 na Faransa.

An sha danganta dan wasan mai shekaru 22 da komawa Real Madrid, kuma Ibrahimovic ya yi imanin cewa lallai can zaifi dacewa da shi.

Da yake shaidawa jaridar wasanni ta Corrier dela Sera, Ibrahmovic yace “Mbappe na bukatar ingantaccen yanayi, kamar na Real Madrid.

Sai dai dan wasan na Sweden, wanda ya buga wa PSG wasanni 180, ya kuma shaida wa shugabannin kulob din na Faransa cewa zai zama wauta muddun suka sayar da Mbappe.

Mbappe ya koma kungiyar ne, a shekarar 2017 a matsayin aro, sai gashi ta sake dauko Lionel Messi a wannan bazarar.

Tawagar Mauricio Pochettino ce ke kan gaba a gasar Ligue 1 bayan wasanni 15 da rashin nasara daya kacal, kuma tazarar maki goma sha biyu ne tsakaninta da Rennes dake biye musu.

No comments