Iran dage akan dole ne fa a cire mata takunkumin da aka kakabata mata. Iran din ta ce ya kamata tattaunawar nukiliyar da aka koma a jiya r...
Iran
dage akan dole ne fa a cire mata takunkumin da aka kakabata mata. Iran din ta
ce ya kamata tattaunawar nukiliyar da aka koma a jiya ranar Litinin tsakaninta
da wakilan manyan kasashen duniya a birnin Vienna, ta mayar da hankali ne kan
batun dage wa kasar takunkumin da aka kakaba mata da kuma tabbatar da cewa
Amurka za ta dawo a cikin yarjejeniyar da aka cimma a baya.
Duk
da wannan fata na Iran, Kungiyar Tarayyar Turai ta ce tattaunawar abu ne mai
cike da sarkakiya.
Tattaunawar
ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka kulla a shekarar 2015, ta sake komawa a
karshen watan Nuwamba, bayan da aka shafe watanni 5 ana tattaunawa bayan zaben
shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi.
Zaman
tattaunawar na neman dawo da Amurka ne, bayan ta fice daga yarjejeniyar a
shekarar 2018 karkashin shugaba Donald Trump na wancan lokacin tare da kara
kakabawa kasar takunkumi.
Gabanin
ci gaba da shirin tattaunawar, Ministan Harkokin Wajen Iran Hossein
Amir-Abdollahian, ya ce ya kamata a sabunta yarjejeniyoyin da kuma tabbatar da
dage takunkumin da Amurka ta kakaba wa kasarsa idan fadar White House ta koma
kan wannan yarjejeniya.
Bude
zagaye na takwas na tattaunawar ya kunshi tawagogi daga Iran da sauran kasashen
da suka rage a yarjejeniyar da suka hada da Birtaniya, Chana, Faransa, Jamus,
da kuma Rasha.
Fadar
White House dai na taka rawa a kaikaice tare da jami'an Diflomasiyya da ke ci
gaba da kai-komo tsakanin bangarorin Iran da Amurka.
Yarjejeniyar
nukiliyar da aka cimma a shekara ta 2015 ta bayar da damar dage takunkumin
tattalin arziki da aka kakaba wa Iran.
No comments