Sabon shugaban Jam’iyyar PDP a Najeriya Farfesa Iyorchia Ayu ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da Jam’iyyar sa ta APC da ...
Sabon shugaban Jam’iyyar PDP a Najeriya Farfesa Iyorchia Ayu ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da Jam’iyyar sa ta APC da su fara tattara komatsan su domin barin karagar mulki saboda abinda ya kira gazawar su wajen samarwa kasar ci gaban da ake bukata.
Ayu ya ce ‘yan Nijeriya sun gaji da rashin iya mulkin da shugaba Buhari da Jam’iyyar sa ta APC ke yi, saboda haka suna bukatar kawar da su daga karagar mulki domin dawo da PDP jagorancin kasar.
Tsohon shugaban majalisar Dattawan Nijeriyan dake kaddamar da sabuwar majalisar zartawar jam’iyyar su ta PDP ya sha alwashin cewar za su sauya yadda ake gudanar da mulki yanzu haka wajen hada kan jama’ar kasa da bunkasa dimokuradiya da gina tattalin arzikin kasar da ya ce tuni ya ruguje.
Farfesa Ayu ya ce za su fadada hangen su da alakar da suke da kasashen duniya fiye da yadda kasar ke yi yanzu zuwa Jamhuriyar Nijar, yayin da ya yi alkawarin shawo kan matsalar tsaro da dawo da martabar Nijeriya a idon duniya.
Shugaban PDPn yayi alkawarin gabatar da jagoranci na gari wajen tuntubar jama’a da kuma gina dimokiradiya a cikin gida domin cimma muradun Najeriya.
Ayu ya shaidawa sauran ‘Yan Nijeriya cewar lemar Jam’iyyar PDP na da fadin da zai iya samarwa kowa matsuguni, a daidai lokacin da yake kira ga wadanda suka bar jam’iyyar da su koma gida.
Ga kasashen duniya kuwa, shugaban PDPn yace suna sane da cewar suna bayyana damuwa akan halin da Najeriya ke ciki, kuma ya sha alwashin cewar ba zasu bari kasar ta ruguje ba kamar yadda wasu suke hasashe.
Ayu ya ce a lokacin mulkin su na shekaru 16, Jam’iyyar PDP ta taimakawa wajen ganin an yafewa Nijeriya bashin da ake bin ta na kudin da ya kai Dala biliyan 30, abin da ya wanke kasar daga basussukan kasashen waje.
Shugaban PDPn ya ce abin takaici ne yadda gwamnatin APC ta sake jefa Nijeriya cikin kangin bashi fiye da yadda kasar take a shekarun baya.
No comments