Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kamfanin Mai Na NNPC Ya Samu Ribar Biliyan 141 A Watan Yuni

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPC ya sanar da samun ribar naira biliyan 141.96 a watan Yunin 2021 idan aka kwatanta da asarar ...


Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPC ya sanar da samun ribar naira biliyan 141.96 a watan Yunin 2021 idan aka kwatanta da asarar naira biliyan 37.46 da ya yi a watan Mayu na shekarar.

Sanarwar da kamfanin ya fitar ranar Lahadi ta bakin shugaban sashen hulɗa da jama'a Garba Muhammad ta ce bayanan hakan na ƙunshe ne cikin rahoton wata-wata na Yuni.

Ana gane riba ko faÉ—uwa ne bayan an ware kuÉ—aÉ—en gudanarwar kamfanin daga cinikin da aka yi na lokacin da ake magana.

Rahoton ya bayyana cewa a Yunin 2021, kuÉ—in shigar da NNPC ya samu ya ragu da kashi 9.07 cikin 100 zuwa biliyan 89.27 daga 894.64 idan aka kwatanta da watan Mayu. Kazalika, ya ce kuÉ—in gudanarwa ma ya ragu zuwa biliyan 299.44 daga 721.93 a Mayun.

Sanarwar ta ƙara da cewa an samu ribar ce sakamakon ƙaruwa da aka samu ta yawan ɗanyen mai da kuma iskar gas da NNPC ke fitarwa.

No comments