Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Karya Ne Sojoji Ba Su Kubutar Da Jami'anmu 20 Ba -Martanin Rundunar Ƴan Sandan Yobe

Rundunar ƴan sandan jihar Yobe ta ƙaryata rahotannin da suka ce an sace jami’anta 20 a wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai ...Rundunar ƴan sandan jihar Yobe ta ƙaryata rahotannin da suka ce an sace jami’anta 20 a wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a ofishin ƴan sanda a Buni Yadi cikin ƙaramar hukumar Gujba kamar yadda BBC ta labarto. 

Rundunar Ƴan sandan ta kuma ƙaryata labarin cewa sojojin Njjeriya sun kuɓutar da su.

“Labarin cewa an sace ƴan sanda 20 a Buni Yadi da kuma kuɓutar su labarin ƙarya ne, domin babu wani jami’i a garin Buni Yadi a ranar da aka ce an kai harin,” a cewar sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan Yobe ASP Dungus Abdulkarim ya fitar

Sai dai sanarwar ta tabbatar da cewa wasu ƴan bindiga da ake tunanin Boko Haram ne ko kuma na ISWAP sun kai hari ofishin ƴan sanda a Buni Yadi inda ƙona ofishin amma babu wanda aka kashe ko aka sace ko ya ɓata.

No comments