Kasar Jamus Ta Yi Sabon Shugaba Olaf Scholz


'Yan majalisar dokokin Jamus sun zabi Olaf Scholz a matsayin sabon shugaban gwamnatin kasar, wanda ya kawo karshen mulkin 'yan mazan jiya na tsawon shekaru 16 karkashin Angela Merkel. 

Olaf Scholz, wanda ya lashe zaben da kuri'u 395 daga cikin 707, zai jagoranci kawancen jam’iyyun SPD, da kuma FDP, kawancen da tuni ya sha rantsuwar kama aiki a wannan Laraba na fuskantar wasu manyan kalubale nan take, wanda suka hada da yaki da annobar korona, sauyin yanayi zuwa rikici da Rasha da Chana kamar yadda rahotanni suka jaddada.

Post a Comment

0 Comments