Daga Ammar M. Rajab Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana cewa; kasarnan tana da kyakkyawan makoma a gaba amm...
Daga Ammar M.
Rajab
Jagoran
Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana cewa; kasarnan tana da
kyakkyawan makoma a gaba amma sai al’umma ta tashi tsaye ta nemi wannan
kyakkyawar makomar daga hannun masu rike da madafun iko da ya bayyana cewa sam
ba su damu da abin da ya dami al’umma ba. Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a
ranar Lahadin 12 ga watan Disambar 2021 a taron tunawa da waki’ar Zariya da ta
auku shekaru shida da ya gabata. Taron ya gudana ne a Yesmin Event Centre dake
Gwagwalada a Birnin Tarayya Abuja. Shehin Malamin ya gabatar da jawabinsa ne
daga gidansa dake Abuja, inda aka haska jawabin ta hanyar majigi.
Tun a farkon
jawabinsa, Shaikh Zakzaky ya fara ne da cewa; “Na so a ce ina tare da ku don na
koya daga sauran mutane kafin na bayar da nawa gudunmawar, amma duk daya; Ina
taya ku murna da kuka taru a yau kan wani al'amari mai matukar muhimmanci a
rayuwar dan Adam - wato batun hakkin dan Adam. Shakka babu, dan Adam an tsara
su rayu a tare, kuma zaman taren ya zame musu wajibi ('yan Adam) ya zama suna da
dokoki, ka'idoji da zai gudanar da rayuwarsu.”
Shehin
Malamin ya ci gaba da cewa; “Kuma mafi muhimmancin cikin dukkannin hakkokin shi
ne ‘yancin gudanar da rayuwa (hakkin kowane mutum ne da ya sami kansa a raye).
Babu wanda zai iya daukar ransa sai dai a tsarin shari'a - ma'ana idan ya dauki
ran wani to lamari ne da ya zama dole shima a dauki ransa, idan ba don wannan
ba, ba za a dauki ran kowa ba”, ya nusasshe.
Har wala yau
Shaikh Zakzaky ya ci gaba da cewa; “Wannan ‘yancin gudanar da rayuwar wanda ya
hada da wasu hakkoki, duk yana cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya, wanda masu
rike da madafun iko a kodayaushe suke rantsuwar kare su. Suna yin rantsuwa da
littattafai masu tsarki wadanda suka yi imani da su (Alkur'ani, da baibul). Kaico, mun samu kanmu a cikin
al’umma a yau, ‘yancin wannan rai din ana daukarsa; wadanda suke rike da
madafun iko suna ganin suna da ‘yancin kashe wani a kowanne lokacin da suka ga
dama, kisan gilla ya zama ruwan dare. Hukumomin tsaro da aka dauke su domin su
kare doka yanzu ana amfani da su (daga wadanda suke rike da madafun iko) domin
karya wannan doka din”, ya lurantar.
“Jami’ai
cikin khakinsu ana aika su su aikata ta'addanci a kan mutane. Sojoji da ’yan
sanda da ma ’yan sandan sirri da ba sa sanye da khakinsu, a gaskiya ma a zamanin
nan suna sanya rigar ta’addanci (ma’ana suna boye fuskokinsu kamar yadda ‘yan
ta’adda ke yi). Gwamnati ta zama makamin aikata ta’addanci, ta koya wa jama’a
su zama ‘yan tashin hankali! An tilasta wa mutane, saboda yanayi, su ma su zama
‘yan tashin hankali (saboda ita ma gwamnati ta zama ‘yar tashin hankali).
“Sakamakon
haka, muna bayani ne kan hakkin dan adam, yakamata mu fahimci cewa wannan
al'umma ba za ta taba kasancewa cikin tsari ba har sai wadanda suke rike da
madafun iko suna mutunta hakkin sauran mutane ba. Masu mulki suna ganin su ne
shari'a- suna ganin su sun fi karfin doka; a don haka za su iya daukar ran kowa
a kowanne lokaci. Ba su damu da yawan magana, wa'azi ko nasiha ba (wanda ake yi
saboda su); ba su damu ba, ba ruwansu da abin da ke faruwa da sauran
mutane”, ya jaddada.
Ya kara da
cewa; “Dubi abin da ke faruwa a cikin wannan al'umma a yau, wanda aka ce kowa
yana cikin yanayin tsoro, ciki har da wadanda suke cikin masu rike da madafun
iko – domin su ma ba za su taba samun zaman lafiya ba idan sauran mutane ba su
samu zaman lafiya ba! A don haka, babban hakkin da kowa ya kamata ya kiyaye
shi, shi ne ‘yancin gudanar da rayuwa, ba ku da ‘yancin kashe rayukan wasu; Ba
ku ma da ikon kashe na ku rayukan- babu wanda ke da ikon kashe kansa. Baku da
‘yancin zubar da ciki saboda da a ce mahaifiyarka ta zubar da cikinka, da ba ka
rayu ba. Babu wanda ke da hakkin ya dauki ran kowa!
“Haka nan,
tun da muna magana ne game da ‘yancin ‘yan adam, akwai hakkin muhalli, hakkin dukkan halittu - ciki har da
dabbobi (suna da hakki). Matattu ma suna da hakki- ‘yancin a girmama su bayan
mutuwarsu tare da yi musu jana'izar da ta dace da imaninsu, dokoki da
al'adunsu”, ya tabbatar.
Har wala yau
Shaikh Zakzaky ya kara da cewa; “Amma a zamanin yau, sai ka ga masu rike da
madafun iko suna tunanin za su iya kashewa tare da kona gawarwakin (mutane), ko
kuma su dauke su zuwa inda ba a san inda suke ba, tare da bizne su a kabarin
bai daya. Kisan kiyashin da ya faru a Zariya shekaru shida da suka gabata
misali ne a nan, inda a cikin kwanaki uku sojojin Nijeriya suka killace birnin
Zaria (ciki har da duk hanyoyin shiga cikin birnin), inda suka kashe sama da
mutum dubu daya tare da kwashe gawarwakinsu. kuma a bizne su a kaburbura
daban-daban. A kan wannan, sun kuma kama mutane kusan dari biyar bisa “zargin
kisan kai” na soja daya. Tabbas, dukkannin kotunan sun sallamesu tare da wanke
dukkan wadanda aka gurfanar da su a gabansu”, ya lurantar.
Ya jaddada
cewa; “Ku dubi yadda masu rike da madafun iko suka so goge hatta hujjojin
wannan danyen aiki da suka aikata. Wannan shi ne mataki na farko da wannan
gwamnati (hukuma) ta dauka, kuma daga baya za ku iya ganin yadda kisan gilla ya
zama ruwan dare a yau. Yanzu mutane suna rayuwa cikin tsoro da firgici a
ko’ina. Ba za ka kashe wasu ba, ka kuma yi tsammanin ka zauna lafiya, sun riga
sun aikata (ta hanyar kisan kiyashin Zariya) sun murkushe zaman lafiya!
“Muna da bukatar
mu sake tunani game da gabanmu; wasu suna tambayata ko akwai wata kyakkyawar
makoma ga kasar nan? Nace akwai! Ba muna rayuwa ne a cikin al’umma marar fata
ba, tabbas akwai fata (ga Nijeriya), amma fatan ya ta’allaka ne a kan mutane ba
akan masu rike da madafun iko ba. Ba mu da fata daga wurin masu rike da madafun
iko, domin ba ruwansu da abin da ke faruwa ga al’umma. Amma yakamata al’umma ta
tashi ta nemi kyakkyawar makoma ga al'ummarmu. Muna fatan nan gaba kadan
abubuwa za su iya sauyawa zuwa kyakkyawa- wannan shi ne fatanmu. Kuma Allah Ya
taimake mu baki daya. Nagode sosai”, ya karkare.
Kamar dai
yadda aka saba a duk shekara ana gudanar da irin wannan taron na tunawa da
kisan kiyashin sojojin Nijeriya wanda suka aikata akan ‘yan’uwa Musulmi
almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky a ranekun 12 zuwa 14 ga watan Disambar 2015,
inda ya fara gudana a Zariya a 2016, sannan aka yi a Keffi dake jihar Nasarawa
a 2017, sai kuma aka yi a Suleja ta jihar Neja a shekarar 2018, a shekarar 2019
kuma, taron ya gudana ne a garin Katsina, inda a shekarar 2020, aka gudanar da
taron a garin Ayingba ta jihar Kogi. A bana ma ba a yi kasa a guiwa ba, a inda
da safiyar ranar Lahadin 12 ga watan Disambar 2021 aka gudanar da gagarumin
taron tunawa da kisan kiyashin sojojin.
Tunda fari
bayan bude taro da addu’a, karatun Alkur’ani mai girma, an gudanar da ‘Display’
daga Kashshaful Imam Mahdi da Intizar da sauran su. An kuma gudanar da wakokin
juyayin munasabar wanda Shamsu Fudiyya da Alhaji Mustapha Gadon {aya suka yi a
lokuta daban-daban.
Farfesa Isa
Hasan Mshelgaru, daga Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, shi ne mai jawabi na
farko a taron, inda ya yi jawabi kan; ‘hujjoji da adadin mata da kananan yara
da sojoji suka yi wa kisan kiyashi a Zariya’.
Malama Ruhi
Rizvi daga Birtaniya ita ce ta kasance mai jawabi na biyu, inda ta yi jawabi
kan; ‘nazarin martanin kasashen duniya kan kisan kiyashin Zariya wanda aka
haska ta hanyar majigi’.
Mai jawabi na
uku a taron shi ne; mai rajin kare hakkin bil’adama, kuma shugaban kungiyar
‘Concerned Nigerians’, Prince Deji Adeyanju, ya yi jawabi a kan maudu’i mai
taken’ “matakan tunkarar take hakkin dan Adam.” Shima an haska ne ta hanyar
majigi. Bayan Deji Adeyanju ya kammala jawabinsa, Farfesa Abdullahi [anladi
daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ne ya yi ta’aliki kan jawabinsa.
Jagoran
Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya gabatar da jawabin rufe
taron, wanda aka haska ta hanyar majigi ga mahalarta taron. A yayin gabatar da
Shaikh Zakzaky (H), wanda Injiniya Abdullahi ya yi, wakilinmu da ya halarci
taron ya lura da yadda wurin taron ya kaure da kabarbari da salatin Annabi
saboda shauki da sauraren jagoran Gwagwarmayar Musulunci.
Dukkanin
jawaban an gudanar da su ne a harshen Turanci. Kuma taron ya samu halartar dimbin
‘yan’uwa maza da mata, yara da kanana daga sassa daban-daban na kasarnan.
Daga karshe, Shaikh Sunusi Abdulkadir ne ya rufe taron da addu’a.
A ranar
Litinin 13 ga watan Disambar kuwa, taron ya gudana ne a muhallin Fudiyyah
Maraba dake karamar Hukumar Karu ta jihar Nasarawa mai makwabtaka da Birnin
Tarayya Abuja. Inda aka saurari waken juyayin wannan waki'a tare da sauraren
bayanai daga wasu daga cikin ganau na waki'ar.
A ranar
Talata, 14 ga watan Disamba, ranar ce a kawo karshen tarukan na kwanaki 3 da
aka gabatar, inda taron ya gudana a garin Suleja ta jihar Neja
dake makwabtaka da Birnin Tarayya Abuja.
Idan ba ku
manta ba, Dandalin Academic Forum, Sisters Forum da kuma Mu’assatus Abdul Fadl
Abbas ne suke shirya taron a madadin Harkar Musulunci a Nijeriya a duk shekara.
No comments