Duba da yadda al'amuran Siyasa da rayuwa suke gudana a Nijeriya, ya zama wajibi na yi kira ga Æ´an uwana matasa na wannan yan...
Duba da yadda al'amuran Siyasa da rayuwa suke gudana a Nijeriya, ya zama wajibi na yi kira ga Æ´an uwana matasa na wannan yanki namu mai albarka (Arewa), kan gwargwadon nazari da Æ´ar fahimtata ko ma iya tunkarar matsalolin da suka addabe mu cikin tanadin magancesu.
Ba tun yau ba, na sha faÉ—a, kuma masana daban-daban sun jima su na nanata muhimmanci da tasirin hadin-kai kan ci gaban kowacce irin al'umma a duniya. HaÉ—in kan da har yau ya gagara samuwa a tsakanin Matasan Arewa, duk kuwa da tulin wayewa da dumbin ilimin da muke takama muna da shi.
A wani zamani da ya shuɗe, an yi wani mutum mai hikima da ƙwarewa da rayuwa, lokacin da wannan mutum ya zo gargarar mutuwa, sai ya tara ƴaƴansa ya kuma raba musu zirin tsinken tsintsiya ya umarci da kowa ya karya nasa, nan take kuwa suka cika wannan umarni na mahaifinsu suka kakkarya wannan tsinke da ya ba su. Bayan dan lokaci, sai ya dauko dafkakkiyar tsintsiyar ya ba wa kowa dami ɗaya ya ce su karya, kowa ya yi iya iyinsa ya karya amma duk suka kasa karyawa. Sai wannan dattijo mai hikima ya dubesu ya ce da su: "wannan shi ne misalin darasin da za ku riƙe wanda ko bayan ba raina zai taimaka muku". Wato, Darasin da yake isar musu shi ne: idan kan ku ya haɗu, babu mai iya karya ku kamar yadda ku ka gaza karya wannan tsintsiya dake haɗe, amma idan ku ka farraƙa to cikin sauƙi za a karya ku, ayi nasarar murƙushe ku, kamar yadda ku ka iya karya wannan zirin tsintsiya cikin sauƙi.
Ƴan uwa Matasa, na kawo wannan ƴar Hikaya ce domin ankarar da junanmu muhimmancin haɗin kai a tsakaninmu, domin shi muke matukar buƙata a yau kafin samun nasarar duk abin da muka Sanya a gaba. Domin rashin haɗin kai, shi ne ummul'aba'isin din taɓarɓarewar tarbiyya da rashin ganin girman manyanmu a Arewa, tayadda za ka ga yaro ƙarami a (Social Media) ya takarkare yana zuba zagi da rashin kunya ga babba, irin matsalolin da zai yi wuya ka samu ga sauran matasan yankunan ƙasarmu.
Haka zalika, mu a karankanmu sai ka iske mu na caccakar junanmu da kalaman batanci saboda bambancin ra'ayin Siyasa, alhali kuwa su manyan da muke yi dan su, kansu a haɗe yake, bambancin ra'ayin Siyasa ba ya raba zumunci ko yanke wata alakar tarayya da ke tsakaninsu, domin har surukantaka suke ƙullawa, wancan ya aurawa dan waccar ƴarsa, da sauran mu'amaloli na zaman tare. Irin kykkyawar mu'amalar da take yi wa Matasanmu na Arewa wahala. Sai dai mu yi ta kashe junanmu da baki da kuma shiga harkokin bangar Siyasa mu na yi wa junanmu ta'addancin da su manyan da muke yi dan su babu ƴaƴansu a ciki. Kuma ko wani abun cigaba ake a ƙasa in ana maganar Matasa, sai dai su shigar da ƴaƴansu da ƴan lelensu su amfana.
Sannan, akasarin Matasan Arewa ba mu da hakuri da jumuri a siyasa, kowane matashi burinsa ya fara nan take ya amfana ita kuwa Siyasa na buƙatar juriya da dadewa ana yi. Haka zalika, ba mu da hadakar ra'ayi da musayar basirar da za mu iya ƙirƙiro da sabbin hanyoyin da ko da siyasa ba ta yi mana rana ba, to za mu amfana ta can har ma mu gina kanmu mu taimakawa wasu. Har wa yau, ba mu iya taimakekeniya ga junanmu ba, ta yadda in wani ya bijiro da tsari mai kyau da zai taimaki al'umma mu rufa masa baya ya kai ga cimma buri ba. Hasali ma idan wani daga cikinmu ya samu dama, sai dai mu hadu muna yi masa hassada da zage-zage gami da 'kananan maganganun wane ya samu ya guje mu, ko in ya ba mun ma bai tsira ba, sai an samu kafar da za a soke shi, mun manta da cewar ni'ima ce Allah ya ba mu, wacce ya kyautu mu rufa masa baya mu taya shi da addu'o'i da shawarwari nagari wadanda za su taimaka da dama daga cikin matasan su sake amfana a sanadiyyarsa.
Ire-iren wadannan matsaloli, su na nan jifge tuli guda a tsakaninmu. Dole sai mun dawo da hankalinmu jikinmu, mu fadawa kanmu gaskiya tayadda za mu kauda duk wani sabani da bambance-bambancen da ke tsakaninmu don samun nasarar hadin-kai mai dorewa a tsakaninmu.
No comments