Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kirsimeti: Almajiran Shaikh Zakzaky Sun Je Coci Taya Murnar Haihuwar Almasihu A Zariya

Daga Ai'sha Suleman, Zariya Almajiran Shaikh Zakzaky dake garin Samarun Zariya sun halarci wani coci mai suna Hekan Church d...


Daga Ai'sha Suleman, Zariya

Almajiran Shaikh Zakzaky dake garin Samarun Zariya sun halarci wani coci mai suna Hekan Church dake Anguwar Hayin Dan yaro a karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna domin taya kiristoci bikin murnar kirsimeti na bana. 

Cikin tawagar ziyarar almajiran Malamin sun mika wa babban Malamin majami'ar mai suna Fasto Hakilu S Darmah kyautar girmamawa dake nuna farin cikinsu da wannan rana ta tunawa da haihuwar Annabi Isa (a.s). 


Bayan kammala gaisawa ne Malamin Majami'ar ya nuna farin cikinsa da jindadinsa da ziyarar tare da karɓansu hannu biyu.


Daga cikin wadanda suka jagoranci wannan ziyara akwai Farfesa Isa Mshelgaru daga jami'ar Ahmadu Bello na Zariya da wakilin almajiran Shaikh Zakzaky na Samaru sai Malam Jamil Basawa da sauran wakilan maza da mata.

Bayan gabatar da wakoki an bayar da lokaci na musamman domin yi wa Shehin Malamin addu'a ta neman lafiya da kariya.

No comments